Manyan Sahabbai – Ubayyu Ibn Ka'b (RA)

Manyan Sahabbai – Ubayyu Ibn Ka'b (RA)

 Manyan Sahabbai – Ubayyu Ibn Ka'b (RA)


Takaitaccen tarihin rayuwa da falala da halayen babban sahabin masoyinmu Annabi  ﷺ Ubay Ibn Ka'ab  رضي الله عنه


Wanene Sayyiduna Ubay Ibn Ka'b رضي الله عنه ?


Lura: Wasu sun ruwaito cewa ya rasu bayan shekara 9 da wafatin masoyinmu Annabi SAW a shekara ta 22 bayan hijira.


Ubay radhiyallahu anhu dan Ka'b ya kasance masani ne, mai kyakykyawan karatun alqur'ani kuma makusancin masoyinmu Annabi ﷺ.


Ya kasance Ansari (Mutumin Madina) kuma dan kabilar Banu Mu'awiyah ne, reshe ne daga cikin sanannun kabilar Banu Khazraj. Ubay bn Ka'b radhiyallahu anhu ya karbi musulunci tun da farko. Yana daya daga cikin wadanda suka fara karbar Musulunci a lokacin mubaya'ar Aqabah.


●Ya halarci dukkan yake-yake har da yakokin masoyinmu Annabi (SAW) bai halarta ba.


Ubay ibn Ka'ab radhiyallahu anhu ya kasance masani ne kuma yana da cikakken fahimtar addini Ya kasance yana bayar da fatawa da (hukunce-hukuncen Musulunci) a zamanin halifancin Sayyiduna Umar Radhiyallahu anhu kuma shi ne mafi shaharar karatun alqurani a cikin Sahabbai baki daya.


● Kuma ya kasance marubuci ga masoyinmu Annabi (SAW). Ya rubuta wasiku kuma a karkashin kulawar masoyinmu Annabi (SAW), ya rubuta wahayin da masoyinmu Annabi SAW ya karba.


●Ubay ibn Ka'ab radhiyallahu anhu yana daya daga cikin sahabbai hudu wadanda masoyinmu Annabi SAW ya kwadaitar da wasu akan su koyi kur'ani daga wajensu kuma da haka ya zama malamin kur'ani ga manyan sahabbai.


● Ya kasance a garin Madeenah ko bayan wafatin masoyinmu Annabi (SAW) ya ci gaba da yi wa addini hidima.


●Ya ruwaito Hadisai da yawa daga masoyinmu Annabi (SAW)


● Ubay bn Ka'b radhiyallahu anhu ya rasu a shekara ta 30 bayan hijira, a zamanin khalifancin Sayyiduna Uthman radhiyallahu anhu.


Lura: Wasu malaman tarihi na ganin cewa ya rasu tun kafin wannan lokacin a shekara ta 22 bayan hijira.


Allah Ta'ala Ya Bamu Lada Mai Girma Akan Dukkan Hidimominsa Ga Rasulallahi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam, Ya Kuma Bamu Ikon koyi Da Manyan Sahabbansa Ta kowace fuska.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post