An gurfanar da jarumar Kannywood Amal Umar a gaban Kotu kan zargin laifi

An gurfanar da jarumar Kannywood Amal Umar a gaban Kotu kan zargin laifi
Amal umar



Rundunar ƴan sanda shiyya ta daya Zone One, dake nan jihar Kano, ƙarƙashin AIG Umar Mamman Sanda, sun gurfanar da guda daga cikin ƴan masa’antar shirye fina-finan Hausa ta Kannywood, mai suna Amal Umar, a gaban kotun majistiri mai lamba 24, dake zamanta a unguwar Gyadi-gyadi.


Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta daya wato Zone One CSP Bashir Muhammad ya fitar.


An dai gurfanar da Amal Umar ne a gaban kotun bisa zargin ta da yunƙurin bada cin-hancin zunzurutun kuɗi Naira Dubu Ɗari Biyu da Hamsin, ga ɗan sandan da ke bincike a kan wani laifi da ake zargin da hannun ta wajan aikata wa.


CSP.BASHIR MUHAMMAD,ANIPR

PUBLIC RELATION OFFICER ZONE ONE HEADQUATERS,KANO.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post