Manyan Sahabbai – Ammar Ibn Yasir (RA)

Manyan Sahabbai – Ammar Ibn Yasir (RA)
Manyan Sahabbai – Ammar Ibn Yasir (RA)



Wanene Sayyiduna Ammar Ibn Yasir رضي الله عنه ?


● Sayyiduna Ammar dan Sayyiduna Yasir da Sayyidatuna Sumayyah, radhiyallahu anhum ya shahara da sadaukarwa da sadaukar da kai ga Musulunci.


Yana cikin Sahabbai da suka karbi Musulunci a farkonsa. Wani abin da ya fi bambamta shi ne ya kasance daga farkon mutanen da suka bayyana Musuluncinsu a gaban kafiran Makka.


● Sayyiduna Ammar radhiyallahu anhu da iyayensa radhiyallahu anhum bayin Abu Huzaifa ne. Bayan rasuwarsa, Abu Jahal ya zama shugabansu.


●Saboda musulincinsu an tsananta musu sosai. Mahaifiyarsa Sumayyah Radhiyallahu anha ta zama shahida ta farko a musulunci bayan Abu Jahal ya kai masa mummunan hari.


Masoyinmu Annabi (SAW) ya taba ganinsu ana azabtar da su sai ya ce musu: "Ku yi hakuri ya iyalan Yasir, lallai makomarku ita ce Jannah!" Haka nan kuma a wani lokaci ya ce “Ya Allah! Ka gafarta wa iyalan Yasir.”


●Ya kasance daga cikin Sahabbai wadanda suka yi sa'a suka yi Hijira. Wasu malaman sun ce ya yi hijira zuwa Habashah yayin da wasu ke cewa ya yi hijira ne kawai zuwa Madeenah.


Ya halarci dukkan yaqoqan da ya yi a rayuwar masoyinmu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, inda ya yi jaruntaka wajen kare masoyinmu Annabi (SAW).


● Bayan wafatin masoyinmu Annabi (SAWW) yaci gaba da yiwa Addini hidima da yakoki da dama.


● Ya zama gwamnan Kufa a zamanin khalifancin Sayyiduna Umar Radhiyallahu anhu, amma duk da haka ya yi rayuwa mai sauki da kaskantar da kai. 


● Ya rasu a yakin Siffin a shekara ta 37 bayan hijira yana dan shekara 93.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post