Hanyoyi Hudu Da Zasu Iya Taimaka Muku Daina Yin Wasa Da Al'aura Idan Kuna Yi

Hanyoyi Hudu Da Zasu Iya Taimaka Muku Daina Yin Wasa Da Al'aura Idan Kuna Yi
Hanyoyi Hudu Da Zasu Iya Taimaka Muku Daina Yin Wasa Da Al'aura Idan Kuna Yi


Yin wasa da al’aura ya zama ruwan dare ga samari da yan mata, wanda babbar barazana ne ga lafiya 


Yin wasa da al’aura na iya zama al'ada, kuma yana yiwuwa ya zama abin alada da ake yi a kullum. Har ma da wasu ma'aurata da suka yi aure ana samun su suna yin wasa da al’aura. Wasu suna kokarin dainawa amma suna samun wahala saboda sun riga sun kamu.


A yau, galibi matasa ko mutane da ba su da aure ne ke yin istimna'i(wasa da al'auar su don biya kansu bukata), kuma wasu mutane suna ganin hakan a matsayin nishadi da biyawa kai bukata. Gaskiyar ita ce, wannan dabia na iya zama matsala idan ka kamu da shi. 


Hanyoyi 4 Da Zaka Iya Taimakawa Kanku Daina Wasa Da Al'aura 


1) Rage Lokacin Da Kake Kasancewa kai Kadai.

Idan ka kana zama kai kaɗai, tunanin aikata istimna'i zai ci gaba da zuwa ranka, yafi kyau ka rage lokacin da kake zama kaɗai. Fita waje, kalli wasanni, yi wasa maimakon kawai ka zauna a daki kai kaɗai. Amma idan baka kebe kaikadai ba bazaka dinga yi tunanin wasa da azzakari ba. Haka suma mata don sune aka fi sanin su da kebewa a waje daya, wanda hakan ke sa su yin wasa da farji. 


2. Daina Kallon Bidiyon Batsa.

Kallon video batsa zai tayar maka da sha'awa, wanda kuma zai yi maka wahala wajen shawo kan lamarin, don da wuya ka kalla ba tare da kaji sha'awar yin wasa da gaba ba. Ya fi kyau ka guji kallon bidiyo irin na motsa sha'awa. Hana kanka samun damar shiga inda za ka kalli hotunan batsa ko bidiyo, jefar da duk wani bidiyo ko abun cikin mujallar da zai tayar maka da sha'awa har ka aikata istimna'i.


3. Ka Kasance Mai Aiki (busy) .

Kada ka taba zama ba tare da aiki ko ka zama kaɗai ba, domin da zarar ka yi haka, tunani da dama zai fara zuwa kanka. Nemo ayyukan da za su sanya ka nutsu kuma su janye hankalinka daga aikata wasa da al’aura. 


Gano sabon wani abin da kake sha'awa da zai dauke maka hankali daga aikata yin wasa da azzakari, kasance mai yin muamala da abokai ta musamman, idan ka sanya kanka cikin aiki(busy), za ka rage damar da za ka yi istimna'i.


4. Gina Dangantaka Mai Ƙarfi Da Allah.

Wani lokacin, za ka samu kanka kana ƙoƙarin daina aikata wannan dabi'a, amma bayan wasu kwanaki ka sake samun kanka kana yin ta. Babu abin da Allah ba zai iya yi ba. Wasu mutane ba sa jin daɗin yin irin wannan aikin, amma ba za su iya daina shi ba saboda sun saba.


Kusantar Allah da karanta Littafi Mai Tsarki na iya taimaka maka daina tunanin yin wasa da al’aura. Yin azumi da ambaton Allah abu ne da zai taimaka sosai wajen daina tunanin aikata istimna'i. 


Gaskiyar ita ce, istimna'i ba abu ne na mutane wanda basuda aure ba, har ma da mutanen da suka yi aure suna fadawa cikin wannan dabia. Don haka aure ba zai iya dakatar da daina yin wasa da al’aura ba a wasu lokutan domin an riga an saba tun kafin auren, ko za'a daina sai ya dauki lokaci. Dole ne ka yi yaƙi da wannan dabia, kuma ka yanke shawarar cewa ba zan kara aikatawa ba, ka yi aiki a kai da ikon Allah. Za ka yi nasara.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post