BINCIKE: Adadin Lokacin Da AKe Bukatar Ma'aurata Su Yi Jima'i A Sati

Amfanin Jima'i 


Masana Sun Bayyana Adadin Lokacin Da AKe Bukatar Ma'aurata Su Yi Jima'i A Sati Don Samun Nishadi Da Kuzari 


Yin Jima'i ba kawai dadi yake samarwa ba, baya ga jindadi da gamsuwa da ake samu Jima'i na samar da lafiya da inganta jiki. Bincike ya tabbatar da cewa yin saduwa akai-akai yana da amfani mai yawa kamar rage barazanar kamuwa da cutar kansa, kara karfin zuciya da rage yawan damuwa. 


A cewar masana Medicalnewstoday, ma'aurata su yi kokarin yin Jima'i a kalla sau biyu duk mako. Domin ana iya samun dalilin yin ayyuka kula da bukatun iyali da sauran ayyukan yau da kullum suna iya tasowa wanda ba lallai a samu yin saduwar aure ba, yana da muhimmanci ware lokutan da za'a gudanar da Jima'i. 


Samun lokacin gudanar da jima'i yana taimakawa wajen kashe gajiya, samun gamsuwa, da kwanciyar hankali a tsakanin ma'aurata. Yana da muhimmanci samun damar gudanar da jima’i don rage abubuwan damuwa. 


Sannan yawa yin Jima'i yana danganta ne da yadda ma'aurata suka tsara da kuma irin bukatar su na yin jima’i. Ana samun miji ko mata idan zai dauki wata ba tare da yai Jima'i ba bazai damu ba, amma dai binciken ya tabbatar da cewa ko da ma'auratan basu damu da yin saduwa ba yana da kyau a duk sati koda sau 2 ne su yi. 

 

Wani bincike da aka gudanar a Jami'ar York a kasar Canada ya bayyana cewa yin jima'i sau biyu a sati yana samar da farin ciki. Amma yawan jimai barkatai baya samar da farin ciki amma yana samar da gamsarwa da kwanciyar hankali, cewar binciken. 


A wani bangaren kuma ma'aurata idan basa yin Jima'i yana haifar da cutuka na rashin lafiya a rayuwarsu. Yana da muhimmanci a matsayin ku na ma'aurata ku san halayyar ku na bukatar jima’i, lokacin da kuke bukatar yi, dadin da zaku samarwa junan ku. 


Daga karshe, yawan yin Jima'i yana da amfani ga ma'aurata, ba wai ana nufin koda yaushe ba, yana da kyau dai lokaci zuwa lokaci ko kuma a kalla sau biyu a sati yin hakan yana samar da jindadi da nishadi da damar kara samun kauna tsakanin ma'aurata. Babban abin bukata dai shine samun gamsuwa a tsakani. 


Ana samun gamsuwar Jima'i ne idan aka fara yin wasanni motsa sha'awar juna da kuma gano abinda kowane yake bukatar a yi masa da yake saka shi jindadi da gamsarwa. Hakan yana kara karfin so da kauna ga masoya. Fatan kun amfana daga abubuwan da kuka karanta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post