Ana zargin Kwamandan Hisbah a Kano Aminu Daurawa Ya Ajiye Mukamin sa bayan sakin Murja

Ana zargin Kwamandan Hisbah a Kano Aminu Daurawa Ya Ajiye Mukamin sa bayan sakin Murja
Ana zargin Kwamandan Hisbah a Kano Aminu Daurawa Ya Ajiye Mukamin sa bayan sakin Murja 

Bincike gaba daya daga shafukan malamin addinin ko na makusantan shi ya nuna babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da murabus din malamin


Tun bayan da aka gano cewa fitacciyar 'yar TikTok, Murja Kunya ta shaƙi iskar 'yanci daga gidan gyaran hali, kafofin sada zumunta suka ɗauki zafi kan maganar. A safiyar Litinin kuma aka tashi da fargabar Kwamandan Hisbah Malam Aminu Daurawa, ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah ta Kano, saboda an saki Murja bayan an aike da ita gidan gyaran hali har zuwa 20 ga October.


Labarin ajiye aikin Aminu Daurawa daga Hukumar Hisbah ya jawo cece-Kuce a social media. Labaran sun nuna cewa sakamakon sakin jarumar Tiktok Murja Ibrahim Kunya daga gidan yari hakan yasa malamin ya ajiye mukaminsa. 


Bincike gaba daya daga shafukan malamin addinin ko na makusantan shi ya nuna babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da murabus din malamin. A iya cewa, farfaganda ce kawai ta mutane, ko da kuwa akwai kamshin gaskiya a ciki to bata tabbata ba tukunna. Duk wani yunkuri ta jin ta bakin malamin kai tsaye ya ci tura. 


Sai dai shafin Freedom Radio Kano na Kafar Facebook ya bayyana cewa, Malam Aminu Daurawa yana nan a Babban Kwamandan Hisbah "Zama Daram Da Kau" - Martani daga Hukumar Hisbah ta Kano ga masu cewa Malam ya yi murabus.


Sai dai mutane da dama na bayyana ra'ayoyinsu inda suke ganin ai kamata yai Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye mukamin nasa, don bai kamata Daurawa ya ci gaba da shugabantar Hisbah ba ma damar ta tabbata Murja Kunya ta fita daga magarkama.


Shin yaya kuke kallon wannan al'amari, kuna ganin ya dace malamin ya ajiye mukamin nasa? Ku bayyana ra'ayoyin ku.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post