Addu'ar Neman Shiriya A Wajen Allah |
Akanso mutum ya yawaita wannan addu'a akai- aka, da yardar Allah duk irin laifin da yake Allah zai shiryar dashi
Wanda ke aikata wani mummunan laifi tsakaninsa da mahalicinsa kuma yakeso ya tuba amma ya gagara. Kama daga sata, chacha, zina, shan giya, da dai sauransu, yana son ya samu nutsuwa. Ko mata da mijinta ke aikata irin wannan mummunan ayyukan to ta tashi ta rinka yin wannan addu'ar, haka miji ma zai iya yi wa matarsa. Anso kayi wanka sannan ka inganta alwalar ka kayi nafila raka'ah biyu ko fiye, bayan ka idar sai ka karanta wannan addu'ar kamar haka;
"اللَّهُمَّ رَبَّ جِبْرَائِيلَ وَمِيكَائِيلَ وَإِسْرَافِيلَ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ عَالِمَ الْغِيبُ والشَّهَادَةِ أَنْتَ تَحْكُمُ بَيْنَ عِبَادِكَ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفِوْنَ اهْدِنِي إِلَى مَا أُخْتَلَفَ فِيهِ مِنَ الْحَقَّ بِإِذْنِكَ, إِنَّكَ تَهْدِي مَن تَشَاءُ إِلَى صِرَاطِ الْمُسْتَقِيمِ"
"Allahumma rabbi jibra'ila wa mika'ila wa israfila, fadiras samawati wal ardi alimil gaibi wash shadati anta tahkumu baina ibadika fima kanu fihi yakhtalifun. Ihdini ila makhtalafa fihi minal haqqi bi iznik, innaka tahdi man tasha'u ila siradil mustaqim"
Akanso mutum ya yawaita wannan addu'a akai- aka, da yardar Allah duk irin laifin da yake Allah zai shiryar dashi.