Addu'a Don Neman Budi Kan Kasuwancin Ka

Addu'a Don Neman Budi Kan Kasuwancin Ka
Addu'a Don Neman Budi Kan Kasuwancin Ka 


 Insha Allah muddin zaka lazimci karanta wannan addu'ar zakaga mamaki cikin hukuncin Allah


Duk wata mu'amala da zakayi ko zakiyi musamman saye da sayarwa, ana bukatar ka dage da addu'a dan neman budi da falala cikin sana'ar.


Ba sai ka wahalar da kanka wajen bin bokaye ko 'yan tsubbu ba, ga wata addu'a muhimmiya da malamai suka ce idan har zaka ko zaki rinka karanta ta duk lokacin daka gabatar da ibada; sallah ko azumi na nafila ko na farilla. Sai ka karanta ta koda sau uku ne ko kuma sau bakwai 7. ko dama sau daya ne yayi. Ga addu'ar kamar haka:


عَسَى رَبَّنَا أَنْ يُبَدَّلَنَا خَيْرًا مِنْهَا إِنَّا إِلَى رَبنَا رَاغِبُونَ" (سَوْرَةُ الْقَلَمِ (32)

Suratul Qalam ayata 32.


Insha Allah muddin zaka lazimci karanta wannan addu'ar zakaga mamaki cikin hukuncin Allah.


Addu'ar Masu Hannun Rariya 

Wani mutum yazo wajen manzon Allah SAW yana gaya masa cewa talauci ya dameshi, sannan da yasa kudi sai su lalace nan da nan, shi baisan me yakeyi dasu ba. Sai Annabi SAW yace masa; da zarar ka shiga gidanka ka rinka yin sallama koda mutum ko babu kowa a ciki. Sannan karka zauna sai kayi min salati sai ka karanta suratul Ikhlas.


Yace dana aikata haka Allah SWT yayiwa arzikina albarka sannan abinda nake samu suka daina lalacewa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post