Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali

Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali
Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali 


Maza gareku, yi kokarin yiwa mace wadannan abubuwan zai saka ta farin ciki


Wannan darasin na yau don maza da ke son su ga mata suna cikin farin ciki ne amma basu san hanyoyin da za su bi don saka mace cikin kwanciyar hankali da jindadi ba. Maza da yawa na tunanin saka mace farin ciki yana da wuya, amma kuma ba haka bane babu wani wuya yin hakan. Hakan yasa na kawo muku abubuwan da Idan Kuna yiwa mata za su kasance a cikin farin ciki. 


Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali 

Ga jerin abubuwan da idan maza na yin su za su saka mata cikin farin ciki da kwanciyar hankali 


1. Ka Taimaka Mata Yin Wasu Ayyukan Ta; Taimakawa mace yin ayyukan gida na sa taji dadi misali shara da goge gida da gyara gado da tsaftace gidan gabaki daya. Koda bata bukaci ka yi hakan ba yi kokarin yin hakan zai sa ta ji kana tausaya mata yin ayyukan gida, hakan zai sa ta yi farin ciki. 


2. Ka Siyo Abin Dadi Lokacin Da Za Ka Dawo Gida; Idan Kana da lokaci da kudi ka tsaya a wani wajen ka siyo mata dan abinda za ka shigo mata dashi gida da zai birgeta. Komai kankantar wannan abin zai saka ta ji dadi sosai. 


3. Yi Kokarin Sakata Farin Ciki; Yi kokarin lokacin da kuke kwanciyar aure ka tabbatar ka fara gamsar da ita kafin ka biya bukatar ka. Yi kokarin yin bincike don gano abubuwan da ake yiwa mace dake sa taji dadi, yin hakan zai sa ta kasance cikin farin ciki da annashuwa. 


4. Ka Zama Mai Kulawa Da Tallafa Ma Ta; Wasu matan suna rashin Sa'a samun maza marasa kulawa dasu, mata na son samun mazan dake damuwa da kulawa dasu da magance musu damuwar su. Mata na son kulawa da nuna musu kauna. 


5. Kulawa Da Bukatun Ta; Da yawa daga cikin maza basa biyawa mata bukatunsu, misali bayar da kudin kashewa, siya ma ta kayan kwalliya, sutura na gida da na fita unguwa. Ka yi kokarin baiwa matarka kudi ko ba masu yawa ba hakan zai sa ta ji farin ciki sosai. 


Yi kokarin yin wadannan abubuwan don ganin ka saka matarka farin ciki, ana samun farin ciki a rayuwar aure idan ya kasance kowa na sauke hakkin dake kansa tsakanin ma'aurata. Da fatan maza za ku yi kokarin tabbatar da farin ciki ga matanku. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post