Yadda Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace

Yadda Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace
 Yadda Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace 


Hanyoyin Yadda Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace Musamman Budurwar Da Bata Taba Yin Aure Ba


Muna yawan samun tambayoyi musamman daga wajen matasa dake shirin yin aure kan yadda za su gane an taba saduwa da budurwa. Hakan yasa muka zurfafa bincike don gano ko ana iya gane alamomin budurwar da aka ta a saduwa da ita.

A iya tsawon binciken da mukai babu wasu alamu na zahiri da suke nuna an taba saduwa da mace, sai dai kuma masana ilimin jima’i sun bayyana wasu alamomin yadda zaka gane an taba saduwa da budurwa amma sai ka aureta zaka iya ganewa. 


Yadda Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace

Idan kana son gane an taba saduwa da mace ranar daren farko zaka ga nonon budurwa a tsaye suke, kuma da wuya kaga sunyi slack sun kwanta. Wannan alama ne dake nuna ba'a taba saduwa da ita ba. Domin kuwa idan an taba saduwa da ita zaka ga sun Kwanta. 

Idan kaga a ranar farko ka sadu da budurwa ba tare da shan wuya wajen shiga farjinta ba alamu ne dake nuna an taba saduwa da ita. Duk da ance akwai wasu dalilai dake jawo mata su rasa budurcinsu ko ba'a sadu dasu ba. 

Sannan sun ce wata alamar na yadda zaka gane an taba saduwa da mace shine nuna kwarewarta wajen iya salon kwanciyar jima’i, domin macen da ba ta ba yin saduwa ba babu wani salon kwanciyar jimai da ta sani. 

Wannan sune wasu daga cikin alamomin yadda zaka gane an taba saduwa da budurwa, sai dai wadannan bayanai ba lallai bane su kasance gaskiya ba domin kuwa wasu matan ko ba'a taba musu nono yana iya zubewa musamman idan manya ne, sannan yanzu tunda zamani ne mata tun kafin aure ana koya musu salon Kwanciyar aure. Haka kuma mata da dama suna rasa budurcinsu ba sai an sadu dasu ba. 

Don haka ku yi watsi da wannan binciken domin babu cikakken gaskiya a cikin sa. Kai dai idan zaka yi aure ka yi shi da zuciya daya, kuma kai kokarin auren mace tagari yar gidan mutunci. Allah ya hada kowa da abokin zama nagari. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post