Abubuwan 8 dake sa mace taso namiji

Abubuwan 8 dake sa mace taso namiji
Abubuwan 8 dake sa mace taso namiji

Wani Bincike Ya Gano Muhimman Abubuwan 8 dake sa mace taso namiji Har Ta Kasa Rabuwa Dashi 


Shin ko kasan cewa da akwai abubuwan dakesa mace taso namiji, Wanne kasani daga cikin abubuwan? Idan kuma baka sani ba ga wasu daga cikin su da muka kawo muku kamar haka:

1 Gaskiya Da Rikon Amana: rikon amana na daga cikin abubuwan dake sa mace tai saurin kamuwa da kaunar namiji. Idan Kana son mace tai saurin yarda da kai da amince maka to ka rike mata amanar kanta da yin gaskiya a cikin Mu'amalar ku. 

2 Tstapta: Babu abinda yafi birge mace wajen namiji kamar tsafta, shiyasa galibi a farkon haduwa da mace idan namiji ya tsare ta a kan hanya abinda take fara dubawa tsaftar Jikinsa idan ta ga mai tsafta ne za ta karbe shi. Don haka Samari a dage da tsafta don fito da mutunci wajen yan mata. 

3 Kalaman So: Idan Kana son ka yi saurin mallakar mace cikin sauki sai ka iya furta kalaman soyayya masu ratsa jiki wanda ko bakwa tare za ta dinga tunawa dakai. 

4 Kyauta: Mata basa son namiji marowaci, duk irin rashin son da mace take yi maka Indai har zaka dinga yi mata kyauta to za ta kamu da Kaunarka. Yi kokari ka kasance mai kyauta ga abar kaunarka don kara tabbatar da soyayyar dake tsakanin ku. 

Misali idan tana bukatar fita dan wajan shan shayi, icecream zai iya samun kofi yaje ayi sticker mai dauke da sunanta, yadda zai birge ta. 

5: Wanda Yasan Mutuncin Kansa, mata suna son samun Namijin da yasan mutuncin kansa da mutuncin macen da yakeso. Hakan yana sa su Kara Kaunarsa da mutun ta shi 

6 Kyau, Hakika mata na son namiji mai kyau Halitta, na tattauna da mata da yawa kan irin zabin namijin da suke so wanda kaso 40 cikin 100 sun fi nuna sha'awar son samun namiji kyakyawa. 

7 Hakuri, babban burin Mace shine samun namiji mai hakuri, duk irin abubuwan da mata suke so daga namiji idan bashida hakuri tafiyar ba za ta yi kyau ba. 

8 Alkawri, cika alkawri na daga cikin siffofin mutum nagari, shine namijin da idan yai magana zai yi wani abun to ba zai saba ba. Idan Kana son samun galaba wajen mace yi kokari ka kasance mai cika alkawri. 

Wadannan sune abubuwa 8 dake saka mace taso namiji cikin sauri, idan har wacce kakeso bata kulawa da kai bata nuna maka kauna to ka tambayi kanka, shin kana yi mata wasu daga cikin abubuwan da muka lissafa?


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post