Yadda Shayin Gahawa Ke Maganin Ciwon Hanta

Yadda Shayin Gahawa Ke Maganin Hanta
Amfanin shayin gahawa


Shan Shayin Gahawa Yana Maganin Cutar Hanta 


Wani sabon binciken Birtaniya daga Jami'o'in Southampton da Edinburgh ya gano cewa shan gahawa na da nasaba da raguwar barazanar kamuwa da cutar hanta da ta tsananta.


Masu binciken sun gudanar da binciken ne kan kusan rabin miliyan na mutanen Birtaniya kuma sun gano cewa masu shan gahawa suna da kashi 26 cikin 100 na rage barazanar cutar hanta kuma kashi 49 cikin 100 na rage barazanar mutuwa sanadin cutar, idan aka kwatanta da mutanen da ba su shan gahawa.


Shan kofin gahawa sau uku zuwa huɗu a rana na da fa’ida sosai kamar yadda binciken ya nuna. Idan Kana fama da cutar hanta yawaita shan shayin gahawa zai taimaka muku wajen magance cutar gabaki daya, a cewar binciken. 


Muna fatan kun amfana daga wannan fatawa na shayin gahawa. Sannan ina fatan za ku yi kokarin sanarwa da al'umma wadanda suke fama da matsalar ciwon hanta, don idan suna shan Shayin gahawa za su samu waraka da yardar Allah.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post