Abubuwa 3 Da Mace Ke Yi Idan Ta Kamu Da Soyayyar Namiji

Abubuwa 3 Da Mace Ke Yi Idan Ta Kamu Da Soyayyar Namiji
Abubuwa 3 Da Mace Ke Yi Idan Ta Kamu Da Soyayyar Namiji 


Idan Mace tana son ka, za ta fara yi ma ka waɗannan abubuwa guda uku


Idan mace ta kamu da son namiji akwai wasu halaye da ta ke yi a zahiri da suke nuna dagaske take son ka. 


Ita mace son ta a Zahiri yake, har idan ta kamu da son namiji to za ka gane cikin sauki domin a Zahiri za ka ga alamu, ita sonta a fili yake nasan duk namijin dake soyayya yasan wannan. 


Abubuwa 3 Da Mace Ke Yi Idan Ta Kamu Da Soyayyar Namiji


Idan har kana son mace kuma ba ka ga wadannan halayen a tare da ita ba to gaskiya ba ta kamu da son ka yadda ya dace ba. 


1) Son Ganinka Koda Yaushe; Babbar alamar da Zaka fuskanci mace na Kaunarka shine koda yaushe tana son ta ganka ko kuma taji muryarka. A kullum za kaga kafin ka kirata sau 1 ita ta kiraka sau 3 ko 5 saboda ka mamaye zuciyarta. 


2) Bata Nuna Damuwa Da Abinda Kake Dashi; Ita mace idan tana son ka babu ruwanta da abinda kake dashi, kullum burinta shine ta same ka, kuma ba za ta taba roko ko neman abu daga gareka ba sai dai Idan kai ne kai niyya ka yi mata. Anan ina kira ga maza da Kada don mace tana Kaunarka ka kakasa yi mata abubuwa na more rayuwa. 


3) Tunanin Aure; Ita mace idan tana son namiji babban burinta shine ku yi aure, za kaji tana yawan baka labarin irin kulawa da abubuwan da za ta yi maka idan kun yi aure. Idan mace bata Kaunarka ba zata dinga yi maka hirar rayuwar da za kuyi idan kun yi aure ba. 


Wadannan sune abubuwa 3 da mace ke yiwa namiji idan ta kamu da soyayyar namiji, ina fatan duk namijin da yake tare da mace mai yi masa wadannan abubuwan da muka lissafa zai kokarin aurenta domin idan ka auri mace dake yi maka wannan soyayyar tabbas za kaji dadin zamantakewar aure. Da fatan Allah ya hada kowa da abokin aure nagari amin 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post