Yadda Ake Gane Alamomin Aljani A jikin Mace

Yadda Ake Gane Alamomin Aljani A jikin Mace
 Alamomin Aljani A jikin Mace


Alamomin Yadda Ake Gane Shigar Aljani A jikin Mace, Da Hanyoyin Magance Su
 

بسم الله الر حمن الر حيم 

Mafiya yawan mata aljanu na tare da su Amma basa iya ganewa sai tsawon lokaci wato bayan tafiya tayi tafiya. Wasu suna nuna kansu da wuri wasu kuma sai anyi aure suke nuna kansu su hana kowa zaman lafiya su tada hankalin kowa, shi kuma aljani Allah yayi shi da karfin sha'awa dan haka abu kadan sai ya burgeshi ya shiga Jikin mace. 


Me Yake Kawo Aljani A Jikin Mace? 

Kafin mu bayyana muku yadda ake gane alamomin shigar aljani a jikin mace za mu bayyana muku wasu abubuwa dake kawo aljani ya shiga jikin mace. Ga su kamar haka 


  • Saka kaya masu nuna tsiraici 
  • Yin wasa a toilet, misali mace ta shiga tana yin wasa da waya ko abinda yai kama da haka
  • Fitar da tsiraici a kowane yanayi 
  • Rashin yin addu'a kafin shiga toilet 
  • Kwanciya babu dan kwali ko rufe gashi 
  • Saka matsatstsun kaya 
  • Rashin yin addu'a a yayin kwanciyar bacci 
  • Yawan yin kwalliya 


   Alamomin Aljani A jikin Mace

Alamomin da mace zata gane tana da aljani a jikinta, gasu kamar haka;


  • Farkin taron mata ana biki
  • Saurin fushi 
  • Yawan Ciwan kai 
  • Jin Haushin mutane ba tare da anyi miki komai ba 
  • Yawan faduwar gaba 
  • Yawan ciwan ciki 
  • Mafarkin ana saduwa dake akai kai 
  • Yawan kai kaiyin ido 
  • Idan samari sukazo gunki basa dawo wa 
  • Yawan fada da miji haka nan 
  • Daukewar sha'awa lokacin Saduwa 
  • Lalacewar maganar Aure akai kai 


Wadannan sune alamomin shigar aljani a jikin mace. Tabbas idan kina yawan jin wadannan alamomin kina da Aljanu, dan haka ki yi kokarin neman magani. Ina Rokon allah ya shiga tsakaninmu da mugayen aljanu ya kauda sharrin su a kanmu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post