Dalilai 10 Dake Kawo Daukewar Sha awa Ga Mata

Dalilai 10 Dake Kawo Daukewar Sha awa Ga Mata
Dalilai 10 Dake Kawo Daukewar Sha awa Ga Mata 


Akwai abubuwa da yawa dake haddasa daukewar sha'awa ga mata kamar yadda masana suka bayyana 


Matan aure da yawa suna korafin cewa basa samun sha'awa, wasu nuna cewa tunda sukai aure su basu San sha'awa Jima'i ba wasu kuma sun bayyana a baya suna jindadin amma kuma sun daina samun jindadin. 


Akwai abubuwa da yawa dake haddasa daukewar sha'awa ga mata, bincike ya gano wasu abubuwa 10 wanda suke jawo mace ta ji bata jin sha'awar jima'i. 


Dalilai 10 Dake Kawo Daukewar Sha awa Ga Mata 

1) Ciwon sanyi na mara (infection) Wannan kam tin_tin nake ta bayanae akansa da irin illolinsa da kuma magungunan. Na kuma yi baya ni mai fadi akan rabe_rabensa Cewa idan akace kinada infection to yazama dole ki fara sanin wanne kike dashi kafın fara neman magani Idan ba haka ba zakisha magani 100 baki warke ba


2) Budaddan farji; Rashin tsukakken farji shima na matukar taimakawa wajan rashin samun biyan bukatar aure


Da zarar ance fatocin bangon farji sun yage ko ace sun bude kuma basu sami kulawa ta musamman ba to wannan matsala zata iya faruwa


3) kaciyar mata; Da zarar an wuce gona da iri wajan yinta to lallae za a iya samun damuwa, don haka dole masu yi su sanda yadda za su dinga ba tare da haifar da matsala ga mace ba. 


4) Magunguna; ko shakka babu a cikin magungunan turawa dana hausa akwai wadanda ke bada gudumuwa wajan lalata sha awar "ya_mace musamman magunguna masu rage tension ko kuma wanda ake amfani daau wajan yin matsi


5) Rashin Samun Ingantaccen Abinci; gaskiya ne rashin cin abinci wanda yadace shima yana rusa garkuwar sha awar 'yamace


6) Saurin Inzali Ga MaiGida; To kai tsaye wannan natsalar tana jinginuwa ne ga 'ya'ya maza musamman saboda rashin karfın azzakari, zai zamana shi namijin baya iya gamsar da ita to lalae hakan zai iya jefata cikin hadari


7) Rashin yin jima in ta hanyar data ke so, da yawan mata akwae nau in kwanciyar da suke so wajan Jima'i, to amma kunya takan hanasu yiwa mazan su  bayani, don basu sani ba kuma hakan na cutar dasu


8) Biyan bukatar kae wato (istimna'i) wannan ma baya bukatar bayani tin da muna da bayanai da yawa akansa idan kun duba Shirye-Shiryen da mukai a baya za ku ji cikakken bayani kan istimna'i da illolin sa. 


9) Jinnul Ashuq; to shima dai munyi bayanai masu tarin yawa musamman alakarsa da ciwan sanyi da yanda yake ga masu infection


10) Rashin sinadaran jima'i ko hawan jini ko kuma wata damuwa me karfi, na daga cikin dalilai dake haddasa daukewar sha awa ga mata. 


To wannan dai sune kadan daga bayanan da nasan suka bayyana kan dalilan dake jawo daukewar sha'awa ga mata. Da fatan duk macen da take fama da matsalar daukewar sha'awa za ta duba abubuwan da aka lissafa tare da daukar mataki.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post