Zamantakewar Aure: Ko Bakada ko Sisi Idan Kana Yiwa matarka Wannan Abubuwan Shiru Za'aji

Yadda Ake Yin Sucking Da Salon Kwanciya A Zamantakewar Aure

Yadda Ake Yin Sucking Da Salon Kwanciya A Zamantakewar Aure 


Zamantakewar Aure: Ko Bakada ko Sisi Idan Kana Yiwa matarka Wannan Abubuwan Shiru Za'aji 


Akwai abubuwan da ya kamata ma'aurata su dinga yiwa junansu a zamantakewar aure da bakowane suke yi ba. A wannan topic na yau mun tattaro muku wasu daga cikin abubuwan da idan miji yana yiwa matarsa a rayuwar aure za ta ƙara kamuwa da soyayyar sa Ga abubuwan kamar haka;


1: Idan tayi kwalliya ka dinga yabawa, "kana kai baby wannan kayan sun yi maki kyau", kalar sa ya fito da kyaun ki.


2: kana yawaita gaya mata kana sonta, ko kuɗi take dashi a asusu zata iya fashe asusun ta baka san kalaman ka sun yi tasiri a zuciyar ta


3: yawaita hira da matarka, tasan damuwarka kasan damuwar ta a zaman aure 


4 : shigowa da ƴar leda koda ta mangoro ce, wanda ya kawo mangoro akwai yakinin idan ya sami kuɗi zai kawo kaji 


5: damuwa da iyayen juna, ta damu da naka iyayen kaima ka damu da nata.


6: ka dinga yaba kitson ta da lalle, sannan idan kaga batayi ka bata kudi taje tayi 


7: ku dinga fita shakatawa tare, idan bakuda kuɗin fita shakatawa ku yi strolling a ƙafa da yamma kuje ziyara daga kai sai ita , ko kuje siyan kifi ko tsire tare kuna hanya kuna hira.


8: Idan kun shiga oza room kuka gama eh yane ka dan rungume ta na wani lokacin kafin ku rabu, ka bayyana mata yanda kaji, ka raɗa mata kalamai masu daɗi a kunne. Idan so samu ne ku yi wanka tare, ka goga mata soso a baya itama ta goga maka.


Ba wai kana gamawa ka ture ta gefe ka tashi kaman wanda ya gama barbara ba, wasu ma wuff suke kaman ana korar su, suna gamawa su shige nasu ɗakin.


9 : Idan tayi maka girki kaci ka yaba, ranar da akayi kuskure gishiri yayi yawa ka sanar da ita cikin hikima.


10 : Idan Kana da lokaci ka dinga taya ta aikin gida, kuyi tare kuna hira sannan idan ta kyautata maka ka dinga sa mata albarka.


Duk namiji mai yiwa matansa irin wannan abubuwan rabuwa dashi zaiyi wahala, ko da kun rabu ta auri wani idan ta tuna wannan kyautatawa da kayi mata za taji kaman tabar wannan ta dawo maka.


Idan kuma rasuwa kayi kullum sai an maka addu'a


Su mata babu abinda muka fi so kaman a dinga ririta su kaman yara, a dinga nuna mana so da kauna, a dinga gaya musu kalamai masu daɗi duk munin mutum bamu ganin munin sa, ko ana kushe ka ita tana son kayan ta.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post