Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, cewar Fati Ladan Bayan Shekara 10 Da Aure

Fitacciyar jarumar Kannywood a shekarun baya Fati Ladan ta bayyana irin rayuwar da ta yi da mijinta tsawon shekara 10 zuwa yanzu inda ta bayyana irin dadin zaman su da irin kulawa da take samu daga wajen mijinta. 

Cikin wata hira da jaruma Fati Ladan ta yi da kafar yada labarai ta film magazine a ranar Lahadi ta bayyana yadda rayuwarta ta kasance tun bayan da ta bar Kannywood ta yi aure. Inda ta bayyana irin yadda ta samu canjin rayuwa tun da ta yi aure. 

Shugaban ƙungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), Alhaji Yerima Shettima shine mijin Fati Ladan wanda yanzu haka suke da ƴaƴa biyu a tsakanin su, A’isha Humaira da Muhammad Shafi’u, kuma su na zaune ne a Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu.

Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, cewar Fati Ladan Bayan Shekara 10 Da Aure
Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, cewar Fati Ladan Bayan Shekara 10 Da Aure 

Fati Ladan ta bayyana farin cikin ta na shafe shekaru 10 da yin aure inda ta bayyana cewa shekara goma ba kwana 10 bane don haka rana ce da take matuƙar farin ciki da Allah ya sa suka kawo tsawon wannan lokaci suna tare.

Ta ƙara da cewa tsawon wannan shekarun 10 da suka yi da mijinta ba komai ne yasa hakan ba sai hakuri da juna da kuma soyayyar juna tun kafin su yi aure. Domin kuwa a zaman aure idan babu haƙuri da soyayya tsakanin mata da miji zaman aure baya tasiri, cewar Fati Ladan.

Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, cewar Fati Ladan Bayan Shekara 10 Da Aure
Ina fatan Allah ya kashe ni a ɗakin miji na, cewar Fati Ladan Bayan Shekara 10 Da Aure 

Fati Ladan ta bayyana cewa ba ta yi kewar masana'antar Kannywood ba domin kuwa babu abinda yafi dacewa da mace kamar aure. Kuma ni na saka a raina aure nake so na yi. Don haka babu abinda yafi mutunci ga mace da ya wuce aure. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post