Yadda Ake Yin Wankan Janaba

Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Saukake

Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Saukake


Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Saukake 


A cikin wannan rubutu na yau za mu kawo muku yadda ake yin wankan Janaba, da fatan za ku yi amfani da hanyar da addinin musulunci ya tanadar. 


Yaya ake yin wankan janaba?

Wankan janaba tana da siffofi guda biyu;


(1) Yanayi da ke isarwa na wajibi, 

(2) Da kuma siffa cikakkiya ta mustahabbi


Amma siffar wankan Janaba da ta ke isarwa ga wanda yayi ta kuma ta wajibi: Itace Bawa ya game jikinsa da ruwa tun daga farkon farawa tare da niyya; Ma'anar wannan Shine bawa ya game jikinsa da ruwa ta kowace fiska yake so tare da niyya. 


Haka zai isar wa mutum; Yayi niyya sai yayi nitso cikin wani kududdufi ko kuma kogi; ta yadda ruwan zai zama ya game jikinsa; Idan ya aikata haka tare da niyya to ya tsarkaka daga Janaba. Amma ita kuma siffa ta biyu cikakkiya ta mustahabbi Itace:


Na farko: Bawa ya wanke tafukansa guda biyu sau uku gabanin tsunduma su cikin ruwa.


Na biyu: Sai ya sanya hannunsa cikin ruwa don ya wanke al'aurarsa da duk wurin da dauɗar janaba ta riga ta taɓa.


Na uku: Sannan sai ya wanke hannunsa da ƙasa ko da sabulu don gusar da dauɗar janaba da ya taɓa da hannunsa.


Na hudu: Sai kuma ya yi alwalarsa cikakkiya irin ta sallah; ma'ana: Ya kurkure baki, da shaƙa ruwa a hanci, ya wanke fiskarsa sau uku, da hannayensa biyu zuwa guiwowinsu sau uku, ya kuma shafi kansa da kunnuwa, sannan sai ya wanke ƙafafunsa sau uku uku.


Na biyar: Sai kuma ya wanke kansa sosai, yana mai shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa; Idan har yayi zaton cewa ruwan ya shiga tushensu sai ya kwara ma kansa kamfata uku.


Na shida: Daga nan; Sai ya wanke sauran jikinsa da ruwa sau ɗaya, yana mai farawa da saman jikinsa, har ya taho ƙasa.


Na bakwai: Idan har kuma ya so zai iya jinkirta wanke ƙafarsa a yayin alwalarsa har sai ya zo ƙarshen wankansa gabaɗaya, sai ya koma gefe don wanke ƙafafunsa.


Waɗannan bayanan zasu bayyana cikin hadisan dake tafe:


Na farko: Hadisin Maimunah (RA), ta ce:


"وَضَعْتُ لِرَسُولِ اللهِ r غُسْلاً وَسَتَرْتُهُ فَصَبَّ عَلَى يَدِهِ فَغَسَلَهَا مَرَّةً، أَوْ مَرَّتَيْنِ -قَالَ سُلَيْمَانُ: لاَ أَدْرِي أَذَكَرَ الثَّالِثَةَ أَمْ لاَ-، ثُمَّ أَفْرَغَ ب

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post