Yadda Ake Tura Saƙon Kalaman So Ga Masoyiya - Android Pols

Rahama Sadau : Yadda Ake Tura Saƙon Kalaman So Ga Masoyiya
Yadda Ake Tura Saƙon Kalaman So Ga Masoyiya


Sakon So Ga Masoyiya: Amincin yabo da girman daraja su kara wanzuwa a gareki sarauniyar Asali


Yau a wannan topic na zo muka da saƙon kalaman so masu ɗaukar hankali da saurayi zai iya turawa budurwar sa su. Waɗannan saƙon so suna ƙara soyayyar namiji ga mace. Ga su kamar haka;

            

 • Amincin yabo da girman daraja su kara wanzuwa a gareki sarauniyar Asali. 
 • Sautin bugun zuciyar mai kaunarki ne ya bayyana tasirinsa daidai lokacin da zuciya ta ɗarsu da soyayyarki. 
 • Kaifin kibiyar so da ƙauna shi ya firgita zuciya daga sukuninta dare da rana zuwa cikin kogin tunaninki koda yaushe. 
 • Laƙanin sirrin dake cikin zuciya ya wanzu da tsantsar rubutun sunanki cikin farar takardar shimfiɗar masaukin soyayya. 
 • Fatan da nake ki karkato da kunnuwanki dan jin sautin kalaman farin cikin da zuciya tayi miki tanadi, tun daga ranar da ta ɗarsu da soyayyarki. 
 • Tambarin sarautar girma da jinjina su tabbata a gareki ƴar gidan haske Asalin haske da kyakkyawar zuciya tagari. 
 • Ina gaishe da kyawawan kumatunki gami da tausasan kalaman furucinki ma'abota tsari. 
 • Hakiƙah kin tabbata Hamshaƙiyar basarkiya wadda ta cancanci yabo ta kowacce fuskar rayuwa. 
 • Allah ya ƙara wadata annuri idanunki da hasken soyayya. 
 • Gwara Ace babu ni da ace na daina Sonki. 
 • Garwashin sonki ya babbake Ruhina abar ƙauna ta. 
 • Gareni baki da Shamaki kinji Autar mata. 
 • Harshena koda yaushe lafazin sonki yake. 
 • Hamshaƙiyar zuciyarki nake burin ki sakani cikinta. 
 • Har Wani shauƙi Nake idan na tuno dake masoyiya. 
 • Idan kina kusa dani bani da sauran damuwa baiwar Allah. 
 • Igiyar sonki tayi min dabaibayi. 
 • Idan babu ke a duniyar nan to nima babu ni. 
 • Jarina shine soyayyarki abar ƙauna. 
 • Jigona itace ƙaunar da nake miki. 
 • Ji nake tamkar a mafarki kin bani soyayyarki. 
 • Kiran sunanki nake ko cikin mafarkin.
 • Kalmomin sonki sune cikon lissafina dare da rana. 
 • Kece mashahuriyar sahiba a gareni baiwar Allah. 

Ina miki Fatan Alkhairi.

Waɗannan sune wasu daga cikin kalaman so da saurayi ko miji zai iya dinga turawa abar ƙaunarsa a koda yaushe musamman idan basa tare da juna. Da fatan masoya za'a kula sosai da waɗannan kalaman.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post