Sakon Soyayya Ga Budurwa Masu Rasta Zuciyar - Android Pols

Rahama Sadau: Sakon Soyayya Ga Budurwa Masu Rasta Zuciya
Sakon Soyayya Ga Budurwa Masu Rasta Zuciya


Sakon Soyayya: Hukuncin Dakika Dauka Akaina Yayimin Tsauri Da Yawa Karki Zama Silar Rasa Wani Bangare Na Jindadin Rayuwata


Wadannan kalaman nuna soyayya ne da saurayi zai turawa Budurwar sa, wanda za su taimaka wajen kara dasa soyayyar sa cikin zuciyarta. Idan mace na cikin fushi furta mata wadannan kalaman za su yaye mata dukkan wata damuwa a lokacin. 


Kece Silar Zubar Da Hawayena

Tunda Kin zabi Ki Azabtar Da Zuciyata Ta Hakan Gashinan Na Zabi Zabin Naki Ina Gudanar Da Kuka Bisa Umurnin Zuciyarki

Matsayinki Yawuce Gaban Ayi Fushi Dake Sai dai Fushinki Yana Girgiza Sassan Jikina Har Yakai Ina Kasa Gano Hankalina Cikin Dogon Nazarin Neman Murmushin ki. 

Itafa Zuciya Tana Biyayyane Ga Zuciyar Datake Yawan So Da Kauna Miyasa Zuciyata Tazamo Abun Azabtarwa Ne Daga Gareki??

Hukuncin Dakika Dauka Akaina Yayimin Tsauri Da Yawa Karki Zama Silar Rasa Wani Bangare Na Jindadin Rayuwata Mana. 

Naji Nabi Kuma Na Aminta Na Amshi Laifin Nawa Shiyasa Nake Neman Afuwa Daga Gareki. 

Mafi Kyawun Lokacin Danake Farin Ciki Shine Lokacinda Nake Kallon Murmushi Daga Fuskarki. 

Ki Yafemin Laifina Ya Mai Saurin Kawarda Bacin Raina Nazo Gareki Na Durkusa Da Guywoyina Agabanki Ina Neman Wata Alfarma. 

Ki Dubi Halin Da Nashiga Sanadin Fushinki Akaina Karki Hukunta Ni Da Irin Wannan Hukuncin Naki Mai Tsananin Kuna Acikin Zuciyata. 

Jarumta Da Saukin Kanki Ne Yasa Bana Son Naga Bacin Ranki Toh Idan Hakane Mezaisa Naso Ganin Fushi Daga Gareki. 

Na Yarda Na Aminta Na Dauki Laifin Na Dorashi Akaina Ki Sassautawa Zuciyata Hakanan Ko Zan Samu Sukuni. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post