Lokuta 13 Da Ba A Son Yin Kwanciyar Jima'i - Android Pols

Lokuta 13 Da Ba A Son Yin Kwanciyar Jima'i

Lokuta 13 Da Ba A Son Yin Kwanciyar Jima'i 


An Bayyana Wasu Lokuta 13 Da Ba A Son Ma'aurata Su Yi Kwanciyar Jima'i 


Idan aka ce akwai wasu lokutan da bai kamata ma'aurata su yi kwanciyar Jima'i ba, nasan wasu za su shiga tunani da rudani, domin za su ji hakan kamar wani sabon abu ne da aka zo dashi. 


Amma ba sabon abu bane sai dai Idan yanzu za ku sani. Domin kuwa addinin Musulunci ya tanadi ladubba ga ma'aurata a lokacin kwanciyar Jima'i. 


1) Na Farko: A dararen mako, daren Laraba ne kawai ba a cika son yin kwanciyar jima’i a cikinsa ba, musamman idan ciki bai riga ya shiga ba. 

2) Na Biyu: Ba'a son ma'aurata su yi kwanciyar Jima'i a daren karamar Salla da kuma daren babbar Sallah (Sallah Layya). 

3) Na Uku: Ba a son saduwa a daren rashin lafiyar Wata (husufi), da na rashin lafiyar rana. Watakila hakan ne ya sa ake son kaucewa kwanciyar Jima'i a daren farko na kowane wata, da daren 15 (daren tsakiya), da kuma daren karshe (daren 29 ko 30) ga kowane  wata na Musulunci, domin mafi yawa a irin wadannan ranaku ne ake yin husufi. 

4) Na Hudu: Ba a son saduwa a daren farko na balaguro (tafiya) tsakanin ma'aurata. 

5) Na Biyar: Ba a son saduwa a lokacin da ake iska (guguwa) mai karfi. 

6) Na Shida: Ba a son yawan kallon farjin mace ko da a lokacin kwanciyar jima’i ne,  amma ba laifi ga sumbata. 

7) Na Takwas: Ba a son saduwa a lokacin da mace ke sanye da kunshi Lalle). Wato irin Kunshin ado da mata suke yi. 

8) Na Tara: Ba a son ma'aurata su dinga yin kwanciyar aure kusa da yaro ko da kuwa jariri ne. Idan za'a yi hakan a yi kokari yi wajen da babu yara. 

9) Na Goma: Ba a son saduwa daga fitowar alfijir zuwa hudowar rana, ko lokacin da rana ta zo tsakiya, ko lokacin da za ta fadi zuwa bacewar shafaki. 

10) Na Sha Daya: Ba a son saduwa da iyali a tsaye. Duk da masana ilimin kwanciyar Jima'i suna ganin yin Jima'i a tsaye wani salo ne da zai iya gamsar da ma'aurata. 

11) Na Sha Biyu: Ba a son saduwa da iyali alhali rana na haska jikinku kai tsaye. Idan da dama an fi son a yi shi cikin inuwa a kebabban waje. 

12) Na Sha Uku: Ba a son Miji da Mata su dinga yin amfani da kyalle guda wajen goge Maniyyin da ke jikinsu. An fi so kowa ya rika amfani da nasa kyalle daban. 


A takaice dai, wadannan sune lokuta ko kuma abubuwa 13 daga cikin abubuwan da ake so ma'aurata su nisanta a lokacin kwanciya Jima'i, don kaucewa wasu illoli ga jaririn da za su haifa. 

Sai dai abin lura anan shine, Musulunci ba haramtawa yai ba,  kuma an karhanta wadannan abubuwa ne musamman ga masu son ciki ya shiga, ko farkon shigar cikin.  (Al-Azkar,  185). Allah  ya sa mu dace.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post