Alamomin Budadden Gaban Mace - Android Pols

Alamomin Budadden Gaban Mace

Alamomin Budadden Gaban Mace 


Alamomin Budadden Gaban Mace Da Hanyoyin Yadda Zaku Kare Kanku Daga Budewar Gaba 


Yanayin halittar gaban mace tamkar robar danko ce wacce zata iya budewa idan aka yi mata talala, haka kuma zata iya komawa ta hade, wato ta tsuke bayan budewa. Tsokokin bangon farji masu motsi ne kuma zasu iya tsukewa ko budewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. 


Budadden gaban mace (loose vagina) ko budewar gaba (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman a lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa ya kara girma, wato ya zama budadden farji, kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki, tsokokin sun saki basu iya damkar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. 


Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri kamar roba marar saukin budewa idan aka ja ta, wasu kuma fatarsu nada laushi da saukin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke budewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa gaban mace na komawa ya tsuke. Duk da haka, farji ba zai taba komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taba haihuwa ba (ko budurwa), koda kuwa anbi hanyoyin magani, gaban mace zai kasance ya kara girma kadan ko da yawa.


Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/karin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan budewar farji tayi yawa yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i. Saboda wannan yanayi na sanya raguwar dandanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin koluluwar dadi (orgasm) lokacin saduwa. 


Dalilin faruwar haka shine, gaban mace baya matse/rike zakari da kyau, ta yanda za'a samu dandanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin wannan guga shine zai kai ma'auratan biyu ga gamsuwa mai karfı a lokacin jima'i. Bugu da kari, wannan matsala na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau.


Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya kara wani aure domin biyan bukatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai dadi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafıya mai daurewa. Matsatstsen gaban mace (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya karawa mace gishirin soyayya mai karfı tsakaninta da mijinta.


Yaya Za'ayi Mace Ta Gane Cewa Ko Tana Da Budadden Gaba? 

1. Mafı yawan mata masu fama da matsalar budadden gaba na fama da matsalar rashin rike fıtsari, wato digar fitsari. Digar fıtsarin zata iya faruwa a lokacin da kika dauki wani abu mai nauyi, ko lokacin da kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba. Yawan shekaru, yawan haihuwa, yawan jima'i, tiyatar likita (karin kofa) ko wani rauni a gaban mace, ko tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga karshe zai iya haddasa budewar tsokokin bangon farji masu matse zakari.


2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai fadi itace: ki saka dan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi kokarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji ba, to zaya iya zama kina da babban gaba. Bugu da kari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo), kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.


3. Idan ya kasance yana da wuya kamin kiji kololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.


4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan bukatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan karami - wato bata jin dadin karamin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafıya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.


5. Idan ya zamanto kina shan wahala kafin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba.


6. Idan ya zamanto sai kin matse ko hade cinyoyin ki biyu sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda karamar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.


7. Idan ya zamanto kina jin karar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake, iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.


Hanyoyin Da Mata Za Su Tsuke Budurwar Gaba

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafıya, wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin sune kamar haka:


1. Motsa jiki, hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara karfı da tsukewa.


Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes (Consultant Obstetrician and Gynaecologist), ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon 'yan dakikoki (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. 


Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacin da kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune, a ko ina kuma a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa'annan zaki yawaita cin Yayan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. 


Wani nau'in motsa jikin kuma shine ake kira  "Kegel exercise". Toh yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fıtsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki rike fitarin, ki danne sa na tsawon dakikoki 10, wato ki kirga 1 zuwa 10 sa'annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau'in motsa jikin na tsuke gaban mace. 


2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai kankara. Yana taimakawa wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa'annan tayi amfani da ruwan sanyin, wato bayan ta koma "normal". Sabanin yanda al'adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace, wasu likitocin a wasu al'adun na ganin yana matse gaba.


3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaban mace sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.


4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafıya.


5. Yunkurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunkuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana rike masa al'aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin haka to zai zama dabi'arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin dadin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post