Sirrin Daren Farko Ga Ango Da Amarya

Sirrin Daren Farko Ga Ango Da Amarya
Sirrin Daren Farko Ga Ango Da Amarya 

 

Sirrin Daren Farko Ga Ango Da Amarya 


Daren farko ko kuma daren angwanci wani dare ne da ake farinciki, idan an wayi gari cikin sa rana ce masoya basa iya mantata domin ranar farin ciki ce a rayuwar aurensu. Za su kasance a wani hali mai tattare da shauki da zumudi na kasance warku a matsayin abu daya daren daraja ga ma’aurata kenan da zarar an kai amarya gidan mijinta ango Kenan. 


Iyayanta da kawayenta zasu barta a daki tana jimamin kasancewar ta a wannan yanayi na zama amarya akan so bayan an watse ambar amarya ta tashi ta dan gyara abin da take ganin ba zai kayatar mata da ango ba. A wasu guraran kawayan amarya suna tsayawa har sai an kawo ango wannan baya cikin al’ada, an fison abar amarya daga ita sai ango. Ango Ya sani abubuwa da yawa ka iya sawa ranar farko ya gaza ganin jini bayan kammala mu'amalar aure da amaryarsa kada ango yasaka a ransa lallai sai yaga jinin domin abubuwa da yawa ka iya ballewa mace murfin budurci ta daga cikinsu akwai. 


1. Jinin haila mai nauyi

2. hawa saman itace ko gini 

3. tsalle-tsalle, kamar wasar tsalle-tsalle da sauran su.

4. Yawan hawan keke ko doki

5. Hawa jaki da dai sauran su.


Yake yar uwa kada kiji na fadi hakan kiyi tunanin ina mara miki bayane domin rufa miki asiri bayan kin gama tonawa kanki. Wannan bayani nawa nayi shine akan wadanda iftila'i ya fadawa suka rasa budurcinsu ba ta hanyar zina ba. Lallai duk macen da ta rasa budurcinta ta hanyar zina duk rufa-rufar da za ta yiwa mijinta sai Allah ya tona asirinta watarana. Kuma a duk lokacin da ya fahimci gaskiya koda kunyi shekaru ne wani abin ka iya dawowa sabo a gurinsa bazai iya jure ganinki tare dashi ba alhalin yana tunanin kafin shi kin san wani da namijin. Daga karshe idan zargi da rashin yadda ya rinjayi zuciyar shi sai ya rabu dake don haka maganin kar ayi to kada a soma. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post