Nasiha Kyauta Zuwa Ga Mata Daga Baraka Bello

Nasiha Kyauta Zuwa Ga Mata Daga Baraka Bello
Nasiha Kyauta Zuwa Ga Mata Daga Baraka Bello 


Nasiha Kyauta Zuwa Ga Matan Aure Har Da Wadanda suke shirin yin auren, Daga Baraka Bello 


Duk Namijin da ya aminta dake ya zabeki a cikin dukkan jerin matan duniya, ya auro ki, tabbas ya kyautata miki zaton zaki kasance mai samar masa da nutsuwa da kwanciyar hankali ne a duk yanayin da zai tsinci kan sa, kuma ya aminta da tarbiyarki ne da har yasa yake son ki zama Uwar 'ya'yan sa. 


Bayan aure duk kin canza, kin daina samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyar sa, kin dawo dashi 3rd-4th class citizen a cikin gidan sa, kin barshi cikin muradi da kaunar ina ma zai samu wacce zata muhimmantar dashi a rayuwar ta, ta zamo dashi 1st class citizen dan gatanta.  


Duk ƙoƙarin da yake yi bakya gani, hirar ku duk ya ƙare a mita da ƙorafi, kullum kina cikin zargin sa. Kullum kina nuna gazawar sa a idon mutane alhali yana ƙokarin sa. Kin dawowa da buƙatarsa ta alaƙar auratayya kamar abune da baida muhimmanci a wajen sa ko kamar alfarma kike yi masa idan ya kawo kan sa. 


Tayaya bazai nisanceki ba alhali ya rasa abunda yake so a wajen ki ? 


Idan ba tsoron Allah yasa a ransa ba tayaya matan banza ba za su dinga dauke masa hankali ba? 


Idan ba tsoron Allah yasa a ransa ba tayaya zai iya sauke hakkin ki na dawainiya da ya rataya a kan sa ? 


Ki yiwa kanki adalci ki duba ta inda kika watsar da mijinki ki gyara.


Wannan shawara ko kuma nasiha kyauta zuwa ga matan aure har waɗanda ma suke shirin auren da waɗanda za su yi anan gaba. Da fatan mata za ku kula kuma ku san abinda ya dace daku.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post