Dabi'u 5 Da Suke Iya Yi Wa Farjin Mace Illa

Dabi'u 5 Da Suke Iya Yi Wa Farjin Mace Illa
Dabi'u 5 Da Suke Iya Yi Wa Farjin Mace Illa


 Dabi'u 5 Da Suke Iya Yi Wa Farjin Mace Illa


Da akwai wasu halaye da dabi'u da mata da dama suke aikatawa wadanda suna iya cutar da farjinsu sannu a hankali ba tare da sun san hakan ba.


Akasarin mata da suke aikata wadannan dabi'un ko dai suna sane suke aikatasu, ko kuwa akwai jahiltar illar abunda suke yi.


Ga wasu dab'iun har guda 5 da suke iya lalata gaban mace domin kula da kuma gujewa aikatasu.


1: Wanke Farji Da Kowani Irin Sabulu- Mata da dama suna amfani da duk wani sabulun wankan da suka samu domin tsaftace gabansu. A maimakon haka suke illata kansu saboda rashin sanin irin sinadarin dake kunshe cikin wadannan sabulan da mata ke wanke gabansu da dasu. Akasarin sabulan dake canza launin fata suna dauke ne da sinadarin da yake yiwa gaban mace illa. Don haka sai mata su kiyaye.


2: Zama Da Jiƙaƙƙun Kaya- Musamman Matan da suke shiga rafi wanka ko tafkin wanka na zamani. Ko kuma ruwan sama ya daki mace har tayi tsamo-tsamo a jiƙe.


A irin wannan yanayin indai mace na zama wani lokaci da jiƙaƙkun kayan a jikinta wannan yana haifara da warin gaba kuma yana iya jawo wa mace illa idan bata kula saboda cututtuka na bacteria da zai iya shiganta. 


3: Kwanciyar Barci Da Matsantsu Wanduna-  Wasu matan suna kwanciya ne da kayan dake matsesu sosai, Wanda yakan hana iska ratsa farjinsu. Wannan ba dai-dai bane. Rashin samun giftawar iska a farjin mace na iya baiwa ƙananan cututtuka daman shiganta. Shi yasa likitoci da dama suke bada shawaran mata su daina kwanciya da kaya a jikinsu ko kuma su riƙa saka Wanduna da zasu sha iska.


4: Yawan shan madaran yogurt ga mata- babban illa ne amma mata dama sun daukeshi abun shansu. A cikin sinadaren da ake haɗa madarar da ita an gano wasu masu ɗauke da sinadaren dake ciki da kai tsaye suke yiwa farjin mata illa. Idan mace tana yawan sha yana iya sa gabanta wari. Madara da cin kayan itatuwa sunfi amfani a jikin mace mace maimakon yogurt.


5: Shan Taba, Wiwi Ko Shisha-  Wadannan nan shaye-shayen kai tsaye na da illa ga lafiyar mace domin hayaƙin da ake shaƙa na iya haddasa illa ga lafiyar mace.


Wadannan sune jerin abubuwa 5 suke iya yiwa Farjin mace illa, da fatan mata za su kula kuma su guji aikata wadannan abubuwan da kan iya jawo musu lahani ga lafiyar farjinsu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post