Abubuwan Da Ya Dace Mata Masu Ciki Su Dinga Ci

Abubuwan Da Ya Dace Mata Masu Ciki Su Dinga Ci
Abubuwan Da Ya Dace Mata Masu Ciki Su Dinga Ci 

Likitoci sun bayyana nau'in abincin da ake so mata su dinga ci a lokacin da mata suke da ciki 


A lokacin da mace ke da ciki yanayin jikin ta da dabi'un ta na canzawa. A wannan lokacin akwai buƙatar ta kula da irin abin da za ta ci domin kare lafiyar ta da na jaririn da ke a cikin ta.


Rashin samun sinadarai masu mahimmanci da gina jiki na iya kawo matsala gare ta ko ga jaririn da za ta haifa. Domin haka a kula da abin da mace mai ciki ke ci kuma a bata abubuwan da take ra'ayi gwargwadon hali.


Masana sun bayyana bayyana irin abincin da ya dace mata masu ciki su dinga ci a lokacin da suke da juna biyu, domin hakan zai kara musu lafiya su da jaririn da za su haifa. Ga jerin abincin da ake so a dinga ci kamar haka:


1. Wake Da Waken Soya.

Wake da waken soya na da sinadaren bitamin wanda ke taimakawa mace mai ciki Karin lafiya ita da jaririn ta, domin suna da sinadarin folate. 


2. Kwai 

Ya nada kyau mata masu juna biyu su rinƙa samun kwai musamman dafaffen kwai. Kwai na da sinadarin choline wanda ke kara lafiyar jikin Mace mai ciki da jaririn ta.


3.  Gero Da Dawa 

Mutane da dama sun fi cin shinkafa da taliya ko Indomie, musamman a kasashen hausawa. Wadannan basu da sinadaran da ake samu a cikin gero ko dawa. Hatsi na da sinadarin bitamin sannan suna kara energy ga mace mai ciki Idan tana sarrafawa tana ci ko sha.


4. Kayan Gona 

Yana da kyau mace mai ciki ta rinƙa shan kayan gona irin su lemu, kankana da Dabino domin bayar da gudunmawa wajen kara bitamin C kuma suna inganta garkuwar jiki. 


5. Ruwa 

A lokacin da mace ta ke da ciki tana buƙatar ta yawaita shan ruwa. Yana yin ciki yana sa ruwan da ke cikin jini ya yi kadan. Shan ruwa nada matukar mahimmanci ga mata masu ciki, amma a tabbatar an samu tsaftatacce.


6. Ganye

Suna gyara jiki da kara jini tare da inganta garkuwar jiki, cin kayan ganye na da matukar tasiri ga mata masu ciki domin yana kara inganta lafiya da Kuzari ga jiki. 


7. Naman Kaza 

Naman kaza ya fi duk wani nama da mace mai ciki zata ci. Naman kaza ya fi naman shanu da na rago kara lafiya ga mai ciki da jaririn ta.


Wadannan sune jerin nau'in kayan abinci da ake bukatar mata masu ciki su dinga ci, da fatan Mazaje za su kula da matansu masu ciki wajen kawai musu irin wannan abincin da muka lissafa. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post