'Yar Gwagwarmaya Layla Ali Othman Ta Dauki Nauyin Yaron Da Mahaifiyarsa Ta WulakantaLaylah Ali Othman ta dauko yaron da mahaifiyarsa take muzguna masa saboda ba shi da lafiya, inda a yanzu zai cigaba da zama a wajenta


Idan za a iya tunawa dai, an ga bidiyon yaron ne a social media, inda mahaifyar tasa take aibata shi da cewar aljani ne ta gaji da rainonsa, maganganu kala-kala na tozarta dan Adam saboda yaron yana da larura, bayan bidioyon ya fita hankalin mutane ya tashi ko ni sai da na yi kuka saboda halin wahala da tsangwama da yaron ke ciki kuma a hannun uwarsa.


Daga karshe Laylah Ali Othman ta ce tana son yaron, a bata shi za ta cigaba da renonsa, inda daga karshe tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Mansura Isa ta je har garin Yola ta dauko yaron daga gurin mahaifiyarsa da ta dinga kuka tana rokon a yafe mata abun da ta yiwa yaronta, yanzu dai Laylah Ali Othman ta karbi yaron ya zama danta za ta kula da lafiyarsa.


Wannan shine yaro na uku da iyayansa suka saki a duniya Layla ta dauka ta rike a matsayin danta ta ke yi musu komai, muna adduar Allah Ubangiji ya saka mata da alkairi, Allah ya faranta mata duniya da lahira amin.


Ga wasu daga cikin hotunan Layla da Yaron Jim kadan bayan da ta wallafa hotunanta dashi a shafinta na Instagram 


Daga Fauziya D. Sulaiman

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post