Tattaunawar jaruma Hadiza Gabon ta janyo cece-kuce a social media - Android Pols

 


Ana cigaba da cece-kuce a dandalin sada zumunta, akan batun tattaunawar da jarumar masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Hadiza Gabon, ke gudanarwa a shafin YouTube, tana gayyato abokan sana'ar ta, tare da yi musu tambayoyi masu zafi, wadanda wasu ganin tambayoyin sun fita daga kwarewar aikin jarida, don kuwa akwai wata jaruma da har sai da ta zubda hawaye a dalilin tambayoyin nata. 


Hadiza Gabon ta sanyawa shirin ta suna "Gabon's Room Talk Show" wanda a baya bayan nan ta tattauna da mawaƙi El-Mu'az, tayi masa tambaya akan alaƙarsa da wata abokiyar sana'arsu, lamarin da ya fusata mawaƙin, har shima ya jefa mata wasu tambaya akan sana'ar da ta keyi da kuma yadda take samun kuɗi. 


Marubuta a shafin Facebook na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan batun, inda mafi yawa ke sukar tsarin da jaruma Hadiza Gabon ke bi wajen yin tambayoyi ga baƙin ta, harma wasu na ganin ya kamata ta nemo kwarewar aikin jarida, domin tattaunawar ba iya ita kadai da baƙin ta ke gani ba, Duniya ce ke kallon su. 


Menene ra'ayin ku? 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post