Mutumin Da Ya Tsinci Kudi Miliyan 16 An Yi Masa Tukicin Aikin Hajji Da Daukarsa AikiMutumin da ya tsinci kuɗi Naira miliyan goma sha shida a hukumar jin dadin alhazzai ta jihar Kano, an masa tukuicin Kujerar Makkah da kuma takardar ɗaukar aiki na din din.


Tun da fari dai mutumin mai suna Ɗangezawa ya bayyana wa gidan Radio Kano cewa da misalin ƙarfe goma na daren ranar Alhamis ya tashi zai tafi gida sai yaci karo da wata leda baƙa a daure, da ya duba sai ya ga ashe Dalar Amurka ce masu yawa nan da nan hankalin sa ya tashi ya dauki ledar ya fasa tafiya gida, ya kwana a ofishin hukumar.


Da gari ya waye ya kaiwa shugaban hukumar Alhaji lamin Baba danbaffa shima hankalin sa ya tashi nan da nan aka bincika aka kuma tarar da ashe kudin guzurin maniyyatan ƙaramar hukumar birnin ne, nan take aka karbi wadancan kudade aka mika su ga jami'in kula da alhazzai na ƙaramar hukumar birnin.


Shi kuwa Ɗangezawa da ya shafe shekaru ashirin da daya yana aikin wuccin gadi ( casual) yanzu haka anbashi takardar aiki ta permanent and pensionable an kuma yi masa alkawarin Kujerar aikin Hajji baɗi idan Allah ya kaimu.


Ina ra'ayin ku game da wannan labari. 

Hussain kabir Minjibir.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post