Kwarin Gwiwa Zuwa Ga Masu Ciwon Hanta ko shawara (Hepatitis)



Cutar hanta cutace wacce ake da ita tun fil'azal kuma take yaduwa cikin al'umma. Wannan matsala ba bakuwar cuta bace.


A wannan zamani wannnan cutar tafi kamari da yaduwa cikin al'umma musamman a kasashenmu masu tasowa. Wannan cuta tana yaduwa kamar wutar daji a wannan zamani.


Sai dai akwai hanyoyin da ya kamata mu sani kuma mubisu Dan rage yaduwar ta dama kawar da ita acikin al'umma. Anfani da alamomi, bayanai da kuma zuwa awon lafiya na daga cikin wani bangaren gano wannan cuta daga bangaren hukumomin lafiya.


Wajibi ne mutane suje cibiyoyin kula da lafiya ayi masu awon wannan cutar, Susan matsayin su daga baya su yi amfani da allurar riga kafin wannan cuta.


Wadannan sune manyan alamomin cutar hanta.

1. Zazzabi

2. Amai da tashin zuciya

3. Kasala

4. Ciwon jiki da kafafu

5. Canjawar kwayar ido zuwan tsanwa

Sai anyi awo ake tabbatar da wannan cuta.


Miliyoyan mutane na dauke da wannan cuta basu sani ba kuma babu wata illa da hakan zai haifar sanadiyar wadannan viruses din. Garkuwar jikin mu na taka rawa wajen murkushe wadannan kwayoyin cuta kullin ta hanyar nakasasu Kowace rana, a haka mutum zai iya cigaba da rayuwa har Allah yai nashi iko.


Ya Ku yan uwa kada samuwar wannan kwayoyin virus a jikinku ya haifar maku da damuwa, tinani ko kuma shiga wani hali na dabam har takai ga lalacewar garkuwar jikinku. Daga lokacin da mutum ya shiga damuwa da tinani zai rasa wasu sanadarai har takai ga nakasu gashi ai nahin garkuwar jikin.


Ya Allah ya bamu lfy, zama lafiya sannan ya kare mu daga miyagun cutuka, wadanda Allah ya jarabta yasa wata kaffara ce ya basu lafiya. 


Babu Wanda zai mutu sai lokaci yayi sannan ciwo ba mutuwa bane.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post