Yadda Ake Soyayya A Cikin Gidan Aure Tsakanin Miji Da Matarsa - Android Pols


Ba duka ne ma'aurata suke yin abubuwan da suke kara musu soyayya da jindadin rayuwar are ba. Akwai muhimman abubuwan da ya kamata su rika yi wanda zai kara musu kaunar juna da zaman lafiya. Ga abubuwan kamar haka;


1. Mace da mijinta su rinƙa cin abinci tare, kuma shi ya rinƙa bata da hannunsa, itama ta rinƙa bashi da hannunta. Wannan yana saka namiji ba zai rinƙa jin daɗin cin abinci a wani wajen ba, haka itama ba za ta iya cin abinci ita kaɗai ba saita jirashi yadawo.


2. Idan zai sha ruwa kada kibarshi yasha da kansa, kaima ka rinƙa bata ruwa da hannanka tana sha kuma a hankali kana rarrashinta. Hakan zaisa duk lokacin da zai sha ruwa a waje ko idan za ta sha ruwa za ku rinƙa tunawa da juna.


3. A wasu lokutan idan kabata ruwan kace kada ta shanye kanaso kasha ruwan dake cikin bakinta, kuma ka haɗa bakinka da nata kasha ruwan daga bakinta, kema ki rinƙa yi masa haka, wannan yana ƙarfafa ƙauna.


4. Miji ya rinƙa sakawa matarsa kaya, haka kema ki rinƙa sakawa mijinki kaya idan kunyi wanka, kuma idan za'a cire kaya ka rinƙa cire mata, kema ki rinƙa cire masa kaya.


Wannan yana sawa ana kasa mantawa da juna a duk lokacin da ɗaya daga cikin ku zai cire kayansa idan baya tare da abokin rayuwarsa zai ji babu daɗi, saboda zaita kowa zaita zumuɗin ɗan uwansa.


5. Ku rinƙa zama a jikin juna idan kuna zaune, ko kuna kallo ko hira, kuma ka rungume matarka koda yaushe idan za ka yi magana da ita, koda kuwa tana cikin halin haila ne, 


6. Haka kema ki rinƙa rungume mijinki a koda yaushe kidaina yin nisa dashi.


7. Wannan yana sawa koda ɗayanku yayi tafiya ya kasa samun nutsuwa har sai ya dawo gurin abokin rayuwasa.


8. Ku rinƙa wanka a tare, kana wanke mata jikinta, itama tana wanke maka jikinka, hakan zaisa bazaku rinƙa ganin laifin junaba.


9. Ka rinƙa goya matarka lokaci-lokaci idan ba tai maka nauyi ba, kema ki rinka goya mijinki lokaci-lokaci idan har bai yi miki nauyi ba. Wannan yana taimakawa wajen kawo zaman lafiya da tausayawa juna.


10. Ka rinƙa bacci a rungume da matarka, kema ki rinƙa rungume mijinki a yayin baccinku, 

 

11. Wannan yana sawa miji da mata basa iya fushi da juna, ko anyi fushi, idan lokacin bacci yayi sai an shirya.


12. Idan za ku yi kwanciyar aure, ku rinƙa farawa da wasanni a ƙalla kamar awa ɗaya ko sama da haka ana wasa da jikin juna, 


Domin wasanni suna taimakawa na miji da mace, su ƙara son juna da ƙaunar juna, kuma yana sawa su gamsar da juna sosai.


13. Bayan an gama kwanciyar aure kuma a nunawa juna anji daɗin juna tare da nuna farin ciki wa juna da kuma godewa juna, da zuga juna saboda yadda kowa ya gamsar da abokin rayuwasa.


14. Idan mijinki zai fita aiki ko kasuwa ki rinƙa rakashi har bakin ƙofar gida kuma ki tsaya ki yi ta kallonsa kina masa murmushi har sai kindaina hangenshi, haka kaima ka rinƙa juyowa kana yi mata kiss akan iska har sai ka daina hangota.


15. Idan kaje gurin aiki ko kasuwa ka rinƙa turo mata da saƙon soyayya ta waya, ko kuma ka rinƙa kiranta kanajin halin da take ciki, haka kema ki rinƙa kiransa kina yi masa addu'a.


Allah ka bamu ikon aiki da abinda muka Karanta. Kuma da fatan masu aure daga cikinmu za ku rinƙa aiki da shawarwari da ake baku.


Mun lura cewa maza anfi samun ƙauyenci daga gareku wajen sakin jiki kuyi rayuwa cikin nisahaɗi da matanku, wannan kuskurene.


ALLAH ya gafarta mana zunubamu baki ɗaya Ameen.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post