Kuskure Ne Kiyi Wadannan Abubuwan A Lokacin Soyayya - Android Pols
Da zarar kin tafiyar da soyayyar ki cikin natsuwa da sanya hankali ba son zuciya ba. Cikin sauki zaki cimma gaci.


Wadannan wasu kurakurai ne da akasarin mata suke yin su a lokutan soyayya to ku guji aikata su, ga abubuwan kamar haka;


1: Mata da yawa da zaran sun fada soyayya abunda suke yi shine yarda da duk wani abunda masoyin nasu ya fadamusu. Ba muna nufin cewa ki rika karyata shi ba. Sai dai a duk wani magana mai mahimmancin da ya fadamiki kada ki dauki wani mataki akansa har sai kin tabbatar da maganar. Rashin wannan yasa mata da dama suke tafka kuskure a lokutansu na soyayya. Don haka a kula.


2: Sau da yawa wasu matan suke cusa kansu ga mazan da suke so. Hakan ba illa bane, sai dai kafin ki cusa kanki wajen namijin da bai gama sakin jiki dake ba a soyayya, ki tabbatar da cewa bai da wata a gefe da yake soyayyar aure da ita.


Wasu matan ba tare da la'akari cewa wanda suka kyalla idanuwa suka ji suna sonshi ko yana da wacce yake so ko kuwa dai shi single ne. Sai kawai su kwallafa ransu a kan zasu aureshi, da zaran kuma ya soma kulata daga baya ya yi aurensa sai a bar mace cikin damuwa. Namijin da kika tabbatar ba shi da kowa, baiyi alkawari da kowacce ba shine abun cusawa kai.


3: Ana samun wasu matan tun a farkon soma soyayya suke nuna burinsu na nunawa wanda yake sonsu isa da gadara na kokarin mallakar sa. Babban kuskure ki nemi nunawa namiji irin wannan kuma a gaban mutanensa.


Duk irin yadda kike tunanin yana sonki ko tabbacin da Malaminki ya baki idan ma asiri kike amfani dashi ba zai yi tasiri ba. Kada ki sake kice zaki rika nunawa namiji mai sonki mallaka da isa har sai kin mallake shi sannan za ki isa da shi.


4: Akwai 'yan matan dake shiga karya a gaban masoyansu a lokacin da suke amsa waya.

Kuskure ne babba ki zama mace mai karya, ko bayan kun gama magana da mutum a waya ki zageshi a gaban wanda ke Sonki. Hakan na iya koran masoyi mai natsuwa muddin ya fahimci cewa kina yiwa wasu masoyanki hakan, shima zai dauka ba zai tsira ba.


5: Akwai wasu matan da suke nuna matsayi a lokacin da masoyansu suke tare dashi.

Macece namiji yake so da aure amma tun kamin ayi nisa cikin hiranta tana nuna masa irin sutura ko man shafawa da sabulun da take amfani dasu ba masu sauki bane. Hatta a ruwan roban da take sha sai wani na musamman. Irin wadannan kalaman ba daga miki aji suke ba illa firgita masoyin naki kawai za ki yi.


Yana da kyau mata ku rika kula da kalamanku, dabi'un ku. Da mu'amalar ku domin kaucewa kurakuren da za su korar muku maneman ku da aure.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post