Wasu Alfanu Da Ma'aurata Suke Samu A Duk Lokacin Da Suka Yi Jima'i - Android Pols




Baya ga lada da biyawa kai bukata. Likitoci sun gano wasu alfanun da duk ma'auratan da suka sadu da junansu za su iya samu domin karin lafiyarsu.


Ga wasu alfanun da zasu iya samu kamar haka.

 

1: Jima'i na magance ciwon kai da warware duk wani matsalar dake tare da jijiyoyin kan bil adama. Wannan yasa koda mutum yana jin ciwon kai da zaran ya gudanar da jima'i sai ya nemi ciwon ya rasa.


2: Ina ma'aurata dake da matsala na numfashi ko cutar asthma. To likitoci sukace ku yawaita gudanar da Jima'i abin zai zo da sauki.


Domin Jima'i yana washe duk wata kofar numfashi musamman hanci da baki.


3: Duk macen da take yawan jima'i zata ga fatar jikinta yana sauyawa, yana haske da sheki. Masana sukace hakan na samuwa ne a dalilin yin Jima'i da mijinta domin hakan na gyarawa mata fatan jikinsu su rika kyalli da sheki.


4: Yawan Jima'i ga ma'aurata yakan samar musu da lafiya. Babu wani motsa jikin da yakai Jima'in mintuna 5 kacal samar da lafiya.


Jima'in da ma'aurata za su yi na mintuna biyar shine motsa jikin da mutum zai yi na mintuna 30 a filin kwallo.


5: Yawan gudanar da Jima'i ga ma'aurata zai magance musu duk wani cuta na fata. Muddin mace na samun Jima'i da wuya fatan jikinta wani kurji ya fito mata. Idan ma ya fito zai bace.


6: Duk wani kitse da kuka ci a wannan ranar muddin za ku yi Jima'i, gaba dayansu zasu kone su bi jiki ba zasu samu wajen zama ba.


Don haka yawan Jima'i yana kona kitsain dake taruwa a jikin mutum idan yaci abincinsa. Da kuma duk wani maiko.


7: Yawan Jima'i nasa jijiyoyin ma'aurata su kasance cikin lafiya a kullum. Yadda Za su rika barin jini yana gudana yadda ake so a jikin mutum.


8: Duk ma'auratan da suke yawan yin jima'i za a samesu suna da yawan sha'awa. Yawan Jima'i na magance matsalar rashin sha'awa.


9: Duk ma'auratan da suke yawan gurzan junansu ba za ka taba samunsu da wani ciwo wai shi hawan jini ba. Saboda yadda a kullum suke yawan motsa jikinsu ta hanyar jiyar da junansu dadi.


10: Ma'auratan da suke yawan jima'i basa kokawa akan ciwon gabobi. A kullum cikin lafiya suke ji a jikinsu komai tsufansu.


Wadannan garabasar masu aure ne kadai kan iya samunsu ta hanyar halas. Kuma su kasance cikin koshin lafiya.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post