Karin Kuzari: 'Yan Uwa Maza Kada Ku Yi Wasa Da Wannan Hadin - Android Pols




Indai kai na miji ne, ko waye kai, ko kafi kowa kwarewa a aikin Likita, kar ka yadda ka zauna baka yin wannan hadin da zan baku. 


Kullum kai ne cin maggi da kayan dandano a girki, kai ne shan kayan zaki da lemon kwalba mai gas, kasha wannan kasha wancan, zaki ya taru maka a mara, baka motsa jiki, kullum kana cikin shan ruwan sanyi, tafiya nan da can akan abin hawa, a gida sanyin AC, a mota sanyin AC, haka a office sanyin AC ke bugaka, sanyi ya mayar maka da gaba kamar lagwanin fitila, tabbas kana cutar da kanka ne dan uwa, Malam ba zaka taba yin lafiya da kwazo ba


A gurin raya Sunnah ta Ma'aiki (SAW) minti biyu kacal ka fado kasa kamar Zakara, Dole matarka ta raina ka, idan ba ta da karfin imani dole ta fara bin mazan banza, wannan hadin da zan baku shine maganin matsalarku 'yan uwa maza. 


Tuzurai bana goyon bayan kuyi wannan hadin, amma ga duk wani tuzuru da aka saka ranar aurensa ya tabbata yayi wannan hadin, yafi duk wasu magunguna da za ka yi amfani dasu tasiri, zai wanke maka mara tas, za ka yi karfi garau:


Kayan Hadin sune kamar haka:


1 Tafarnuwa 

2 Kajiji 

3 kanumfari 

4 citta danye mai yatsu.


Za'a bare tafarnuwan, cittar za'a tsagata gida biyu, sai a wanke kajijin da kanumfari a cire kasan dake jikinsu, sai a hadasu gaba daya a zuba a cikin bokiti ko wani roba mai murfi da aka cikashi da ruwa mai tsafta, a barshi sai yayi kwana daya kafin a fara sha. 


Duk lokacin da kasha kofi daya sai ka sake zuba ruwa cikin kofi daya a kai, haka za'a dinga sha kowani lokaci har sai dandanonsa ya kare, a kalla duk bayan wata biyu kayi wannan hadin, kudinsa ba zai wuce dubu 2 ba


Don Allah dan uwa Magidanci ka kasance mai yawan yin wannan hadin.


Idan da matarka tana maka raini za ta dawo yi maka ladabi da biyayya, idan ka fita daga gida duk bayan awa daya za ta kiraka ta tambayi lafiyarka, damuwa take ka dawo gida, kai karan kanka zaka san cewa kai yanzu na miji ne ba mata-maza ba, babu sauran raini kuma


Muna fatan Allah Ya kara mana aminci da zaman lafiya tsakanin mu da matan mu na Aure.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post