Mata 'Yan Madigo
Madigo wato lesbianism a turance, wata hanya ce da mace za ta biya bukatarta ga ‘yar uwarta mace, ta hanyar sumbatar juna, shafe-shafe, rungume-rungume, da duk wani abun da zai kwantar masu da sha’awar su ko kuma ya gamsar da su, ba tare da kusantar da namiji ba.
Mafi yawan matan da ke da wannan dabi’ar suna afkawa ibtila’in ne a sanadiyar kawance da masu irin dabi’un, wasun su kan fada ne a sanadiyar kwadayin abin duniya, wasu rashin yin aure da wuri, wasu kuma zazzafar alaka ta kawance; inda wasu kuma rashin gamsuwa da mazajensu, musamman masu auren cikinsu; amma wasu jaraba ce kawai da bala’i suka dorawa kansu da kansu.
Wannan salon zina ta hanyar madigo dai kusan zan ce ta samo asali ne shekaru masu yawa da suka shude 1464-1526, daga kasar Girka, ta hanyar wata shahararriyar mawakiya kuma ‘yar gwagwarmayar nema da kuma kare ‘yancin mata ‘yan uwanta, mai suna Sappho.
Saboda jajircewarta akan kare ‘yancin mata, sai ya kasance duk inda Sappho ta je ko za ta je, za ka samu mata ne zalla zagaye da ita, dalili kuwa shi ne yadda take wake-wakenta gabadaya suna takalo wa mata da wani maganadisun sha’awar junansu ne, ma’ana wakokin da take rerawa kamar ishara ne ga matan da ke sauraron wakar ga neman ‘ya’ya mata ‘yan uwansu ya fi neman jinsin maza. Sannan tana rera wakar cikin sigar sha’awa da yanayin takalo wa matan da ke zagaye da ita sha’awarsu.
Da yake ita Sappho malamar makaranta ce kuma wadda ta taso a gida mai tarin dukiya a tsibirin Lesbos da ke Girka; hakan ya sa ta dinga koyar da yara dalibai kowace iriyar fitsara da tambada cikin sigar wake-wakenta na madigonci; tarihi ya nuna cewa ta yi sanadin lalata kananan yara ‘yan mata fiye da misali, kuma ta rinjayi mata da dama ta hanyar wakokinta, da yake ta kware ainun wajen tsara waka a wancan lokacin.
Sappho ta rubuta wakoki sama da dubu 10,000, duk da yanzu tarihi ya nuna cewa wakokin duk sun bata a doron duniya, dangogi 630 ne kacal suke cigaba da gudana a fadin duniyar, wadanda kuma kaitsaye kalamai ne ko baitoci ne da duk manazarta tun a wancan lokacin irinsu Lawrence Alma-Tadema da Friedrich Gottlieb Welcker har zuwa yanzu suka bada tabbacin Sappho ba mace ba ce wacce take sha’awar da namiji ko son kusantar shi da sunan kwanciya ko jin dadi; baitoci ne da karara suke nuna tsantsar kauna da shaukin yin mu’amala da ‘ya’ya mata ya fi dadi da samun natsuwa a zuciya fiye da da namiji a cikin wake-wakenta.
Saboda haka ne kuma tun daga waccan lokaci mata suka yi ta kafa kungiyoyin neman ‘yancin kansu, wanda a turance ake kira ‘Feminist Mobement’. A yau ko’ina ka je a kasashen duniya za ka samu irin wadannan kungiyoyi; wasu ana kafa su ne da zahirin manufofin madigo, wasu kuma ana kirkirarsu da kyawawan manufofi a bayyane, amma a manufofin boye sai kina ciki za ki fahimci manufofin sun sha bamban da yadda mutane suke kallo a zahiri, irin abun nan ne wai badda-bami, waje fari, ciki kuma baki.
Wasu kungiyoyin kuma ana samun wasu gurbutattu ne da suke fantsama dabi’ar a tsakaninsu, sai ya zama a kwana a tashi kungiyar ta rikide ta canza manufofinta na zahiri zuwa manufofin boye.
Ire-iren wadannan kungiyoyi sun fi yawa a kasashen turawa da yankin Asia; ta kai yanzu muraratan wasu tambadaddun mata da hadin gwiwar wasu cibiyoyi da kungiyoyin kare hakkin mata suna yekuwar majalisar dinkin duniya ta ware wata rana guda da za ta zama ranar ‘yan madigo, luwadi da kuma mazinata ta duniya (LGBT). Astagfirullah!
A wannan zamani da muke ciki yanzu kuwa, zinar madigo ta wanzu kusan ko’ina, musamman a rukunin kungiyoyi, ofisoshi, ma’aikatu da makarantun kwana da kuma dakunan dalibai mata. A inda wannan wuri ya zamo tamkar cibiya ce ta wayar da kan dalibai mata, musamman kanana, wadanda ke da kananan shekaru ko sababbin zuwa.
Ba wai ina son batawa ko kushe makarantun kwana ba ne na maza ko na mata zalla, a’a sai dai kawai ina son nuna yadda abubuwa suka lalace, tarbiyya ta tabarbare ta zama abun wahala, malaman makaranta da kansu suna neman yara da wannan dabi’ar, tun daga kan makarantun mata har mazan. Malamai da dalibansu nawa aka kama da laifin aikata masha’a? To ka san me diyarka take yi da diyar wani a cikin dakunan kwanansu? Ko ka taba tambayar diyarka mene ne ma’anar ‘Daughter’ da suke yi a makaranta?
To malam gaskiya ka sani a yanzu madigo ya zama ruwan dare game duniya, domin kuwa kowane bangare na mata ya riga ya afka, duk da yake karuwai ne suka fi aiwatarwa, amma ‘yan mata matasa su ne na biyu a yawan masu wannan harkar.
Zawarawa na yi matuka; amma mafi sharri da muni tare da yin Allah-wadai daga cikin masu wannan harkar su ne matan aure, wadanda ke da mazajen sunnah a gidajensu, amma sun dulmiya tsundum cikin wannan harkar; ba sa sha’awa ko son kusantar mazajensu na sunnah sai don dole, sannan zaman aurensu tamkar fakewa da guzuma suke suna harbin karsana, amma suna fita waje ko su kawo abokiyar harkarsu har kan gadon mazajensu don gamsar da kawunansu.
Harkar madigo tsakanin matan aure, ko matar aure da bazawara ya fi kowanne muni da hatsari, saboda su sun fi nuna bakin kishi a tsakaninsu; suna kulla aure ne a tsakaninsu kamar miji da mata, miji shi zai dinga yi wa matar duk wata hidima da kashe kudi irin na garari da gadara don gudun kar ta kubuce mata ta je ta nemi wadda ta fi ta.
Shin ya za ka ji kai dan uwana mai karanta wannan rubutu a daidai lokacin da ka taras da budurwarka ko matarka ta sunna tana zantawa da wani kato ita kadai a cikin daki? Na san za ka ce sai inda karfinka ya kare ko? To wallahi mace mai neman ‘yar uwarta mace idan ta kama abokiyar harkarta ko abokiyar aurenta, matukar akwai wuka ko wani makami a hannunta za ta iya kashe daya daga cikinsu har lahira, saboda bakin kishin juna da suka sa a zukatansu.
Matan aure da yawa sun saka kansu cikin wannan mummunar dabi’ar, matarka tana sanar da kawar harkarta duk lokacin da kake fita da kuma lokacin da kake dawowa daga office ko kasuwa; saboda haka kafin ka dawo waccan ta zo sun gama abin da za su yi; shi ya sa kai ka zama tamkar fanko a wajen ta.
Bari don Allah in maka wata tamba. Shin ka taba tuhumar matarka dalilin da ya sa kake ganin kawarta kullum a gidanka? Ko kuma ka taba tambayarta abin da take zuwa yi kullum gidan kawarta Jummai ko Indo? Ko kuwa kai a matsayinka na uba ka taba bincikar diyarka alakarta da kawar nan da suka yi shakuwar fiye da kima? To wallahi ina bada shawara a dinga bincike da kuma sa ido, domin sau tari iyaye suna kokarin tarbiyyantar da ‘ya’yansu amma wasu suna rusawa.
Nan gaba idan Allah ya bani dama, za mu yi kokarin duba illolin madigo ta fannin lafiya, addini da mu’amala. Idan hali ya yi kuma zan bada wani labari da wata matar aure kuma ‘yar madigo ta fada min da bakinta, amma kafin nan ga kadan daga alamomi da dabi’un ‘yan madigo.
1. Macen da take bayyanawa ‘yar uwarta mace tsiraicinta.
2. Macen da ke yaba kyawun ‘yar uwarta mace ta fuskar sha’awa.
3. Macen da ke rungumar ‘yar uwarta mace ko sumbatarta da nufin wasa.
4. Macen da take nunawa kawarta bidiyon ‘yan madigo.
5. Macen da za ta kama hannun mace ‘yar uwarta ta dinga shafawa babu wani dalili
6.Ko Macen da za ta dinga shafa gashin kan kawarta.
7. Mace mai lazimtar kwanciya kan cinyar mace ‘yar uwarta ba tare da dalili ba.
8. Macen da a kodayaushe take son ganin surar jikin mace ‘yar uwarta.
9. ‘Yar madigo tana da yawan son yin kyauta ta bajinta da ban mamaki ga wadda ta gani tana so.
10. Yana daga cikin alamomin ‘yan madigo kebancewa kuryar daki su kadai.
11. ‘Yar madigo ba ta da wata hira sai ta mace ‘yar uwarta.
12. Suna kyamatar yin mu’amala da namiji, ba su damu da yin saurayi ba.
13. Suna da sha’awar kallon fina-finan batsa, musamman na ‘yan madigo.
13. Suna matukar zama a gidan da mata ne zalla, kamar zawarawa da ‘yan mata.
14. Macen da ke tube rigarta a gaban mata ‘yan uwanta ba tare da jin kunya ba.
15. Mace mai yawan son shafa nono ko taba mazaunan kawarta maimakon musabaha.
16. Suna yawan kiran junansu da ‘Sweety’ ko ‘Darling’ ko ‘Dear’ ko kuma ‘My Lobe’.
17. Suna da son yin dinki matsattse mai bayyana dukkan surar jikinsu.
18. Sun iya yin fari da idanu don janyo hankalin macen da suke so.
19. Sun fi koda kyawun mace fiye da namiji
20. Suna da bakin kishi
21. Suna da son yin tsabta ta kece raini.
22. Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka.
23. Suna son saka sarka a kafarsu da zobe a yatsan kafar (Duk da an mayar da shi ado yanzu)
24. Suna son saka zobe a babban dan yatsan su na hannu.
25. Yawancin su suna son kara tsawon gashin idonsu ko shafa masa kala.
26. Suna auren junansu kamar yadda namiji ke auren ‘ya mace.
27. Shakuwa mai tsanani tsakanin mace da mace, barci kawai ke raba su.
28. Mace ta mayar da gidan kawarta kamar wurin aikin ta, kodayaushe tana zuwa gidan.
29. Suna ba junan su abinci a baki kamar yadda mata da miji ke yi.
30. Suna tausasa lafazinsu yayin amsa wayar wadda suke harka tare ko suke so.
31. Sukan biya wa junansu bukata ta hanyar kiran waya ko hira a kafar sada zumunta.
32. Ana gane su ta hanyar hotunan mata da suke ajiyewa a wayoyin su.
33. Suna kulla mummunar gaba ga duk macen da take nema ta yi musu kwacen kawa.
34. Suna yawan daga gira ko yin kifce wajen nunawa ‘yar uwarsu wadda ta kwanta a ransu.
35. Suna da yaren da suke yi a wajen hirarrakin su, ta hanyar kushewa ko yaba junansu.
36. Masu auren cikinsu suna yawan tafiye-tafiye (ko mazajensu) da mu’amala da manyan mata.
37. Ba sa gamsuwa da da namiji sai sun ayyana yadda suke saduwa da abokiyar harkarsu.
38. Suna tsanar aure duk sanda aka yi musu maganar shi.
39. Suna da kalaman gane juna, irin ‘Muna tare’, ‘Kin tayar min da tsumi’, ‘Za ki yi dadin harka’.
40. Suna son amfani da kwayoyin da za su fitar da cikon halittarsu, kamar kirjinsu da mazauni.
41. Yawancin masu auren cikin su ba sa son haihuwa.
42. Mace ‘yar madigo tana nesanta kanta ga kalaman batsa ga namiji, kuma tana kame kanta.
43. A kafafen sada zumunci suna dora hoton kafa, harshe ko kuma leben mace da sauransu.
44. Suna sha’awar saka dankunne ko wata sarka a hancinsu (Duk da an mayar da shi ado).
45. Ba su damu da kulawa da kuma nuna kishin mazajen su ba.
46. Idan suna kallon fina-finan turawa sun fi mayar da hankali kan matan.
47. ‘Yar madigo ba ta sanya kumbar kanti, kuma ba ta barinta ta yi tsayi a ‘yan yatsunta.
48. Wasun su suna rage gashin kan su kamar na maza kuma suna sa masa kala.
49. Suna yin zanen tatoo mai kusurwa uku (triangle) a hannu ko kafarsu.
Allah Ya Shirya Su Da Kuma Mu gabaki daya amin.