Yau na zo muku da wani sabon hadi na ma'aurata musamman mata domin Karin samun ni'ima da dandano wajen maigida.
Za ki nemi kayan hadi kamar haka:
1. Gurjajiyan kwakwa
2. Ruwan tafasashiyar kanunfari
3. Garin dabino
4. Garin soyayyan ridi
5. Nono
6. Zuma
Bayani: Za ki samu wadannan kayan hadin da muka ambata, sai ki hadesu guri daya ki gauraya ki markada ki tace ki zuba nono da Zuma ki juya ki dinga sha.
Karin Ni'ima Da Gamsar Da Maigida:
Za ki samu kankana ki markada a blender ki saka garin ridi aciki da madara da zuma ki zubawa oga yasha kisha.
Maganin Sanyi Infection:
Hulba yana mutukar kashe kwayoyin cuta da hana zuban ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko ɗiban garin a haɗiye da ruwa ko yoghurt yana mutuƙar kashe kwayoyin cuta. Haka a jiƙa da ruwa na minti ko a dafa a rika tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe cututtukan sanyi.