Maganin Jin Zafi A Yayin Jima'i - Android Pols




Tambaya 

Assalamu alaikum. Da fatan malam na nan lafiya ya aka ji da iyali da hidindimun rayuwa, Allah yayi mana jagora ala kulli halin.


Da Allah malam ina neman taimako ne, ina yawan samun matsala wurin mu'amala ta aure tsakani na da miji na. idan mun gama har gabana faduwa yake saboda tsabar zafi, kamar an saka mun yaji dan zafi. yakan yi kwana 2-3 ina fama da hakan. ko menene dalili? Sannan kuma da Allah a taimaka mun da magani. 


Amsa 

Wa'alaikussalam wa rahmatullahi.

Jin zafi yayin jima'i ko bayansa, yawanci yakan faru ne ta sanadiyyar wasu kwayoyin cuta dake tare da farjin ita macen.


A wasu lokutan kuma idan Mace tana da Jinnul Ashiq (Aljanin Soyayya) irin wanda ke zuwa yana saduwa da mace a cikin barci, to shima yakan haddasa wa mace bushewar gaba, daukewar sha'awa, rashin ni'ima, jin zafin jima'i, da sauransu.


Ki samu garin Habbur Rashad kullum kina dafa cokali biyu a cikin ruwa kofi daya. Idan ya tafasa sai ki juye a babbar roba ki surkashi daidai gwargwadon yadda ba zai kona jikinki ba, sannan ki rika shiga cikin ruwan kina zama har tsawon minti 10 ko 15.


Sannan ki samu wani garin nasa kina shan cokali guda (teaspoon) a cikin madara kullum. Sannan kina shafa MUHRIQUL JINNI a jikinki yayin da za ki kwanta.


To in sha Allah za ki daina jin zafin. Kuma ko da akwai sauran matsalolin tare dake za ki samu lafiya. Ko da kina mafarkin saduwa dinma za ki daina in sha Allah.


Allah ta'ala yasa mudace


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post