Sabon bincike ya musanta cewa ɗan'adam ya samo asali ne daga Afirka - Android Pols
Masana kimiyya a ƙashashen Canada da Amurka sun wallafa wani bincike da ke ƙalubalantar bayanin da ke cewa ɗan adam ya samo asli ne daga nahiyar Afirka.


Masanan na jami'ar Mcgill da jami'ar California - Davis, waɗanda suka yi bincike kan ƙwayoyin hallita, sun ce akwai al’ummomi da yawa da ke rayuwa a ɓangarori daban-daban na Afika, suna hijira daga yanki zuwa yanki kuma sun kwashe dubban shekaru suna cuɗanya da juna.


Wannan bayanin ya ƙalubalanci tunanin da ake yi cewa ƴan adam na da asali guda ɗaya da ke gabashi ko kudanacin Afrika.


“A lokuta daban-daban mutane sun amince da bayanin cewa ƴan adam na da asali guda ɗaya, suna da yaƙinin cewa ƴan'adam sun samo asali ne daga gabashi ko kuma kudancin Afrika” a cewar Brenna Henn, wata mai bincike kan kwayoyin hallita a Jami’ar California da ke Davis, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka wallafa binciken.


Amma an samu cikas wurin samun matattara kan waɗannan bayanan da yake babu isassun shaida da aka samu daga ɓurɓushin hallitu na kasancewan ƴan'adam a ƙasashe kamar su Morocco da Habasha da kuma Afrika ta kudu da za su nuna cewa ƴan'adam sun yi shekaru dubu ɗari uku suna rayuwa a nahiyar Afrika" a cewar ta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post