Maza Ku Daina Auren Matan Da Suka Fi Karfin Ku - Android Pols
A gaskiya akwai cutarwa matuka kaga namiji ya auro mace Kyakkyawa, shekara da shekaru iyayen ta sun kula da ita, amma yana aurenta  bayan wani dan lokaci sai kaga duk ta lalace, kyan ya tafi, ta rame, babu kuzari kwata-kwata a jikin ta.


To me yake kawo haka?

A zahiri akwai mata wanda zaka ga cewa suna kula da kansu sosai kafin suyi aure. Kuma daidai gwargwado suna jin dadin a wajen iyayen su. Toh amma da sun yi aure sai hakan ya chanja saboda shi wanda ya aure sun bazai iya dorawa a inda iyayen ta suka tsaya ba.


Wani namijin akan kudin gyaran jiki irin su kunshi, gyaran gashi, kitso da sauran su, sai a rika hawa sama da shi. Gani yake idan ya bata ci, sha, sutura, shikenan ya gama sauke nauyin da Allah ya dora masa. Idan yarinya mai dan son ciye-ciye ce, irin su snacks, sweets, kaza da sauran su, sai kaji yana cewa ni fa bazan iya ba.


Maganar gaskiya shine dole kayi compromising a irin wannan yanayin. Ita mace sai da gyara. Ita mace sai da kashe kudi. Idan har kana so tayi kyau, tayi tsaf da ita, sai ka kula da wannnan sashe. Hakanan idan mai kwadayi ce, dole lokaci zuwa lokaci ka rika kawo kayan kwadayi, ba wai kullum ba.


Kayi daidai gwargwadon budin ka. Dan uwa idan har duk sati ko sati biyu zaka kai motar ka car wash a wanke, kaje service karshen wata, toh ita motar ta fi uwar yayan ka ne? Ita motar tafi mai dakin ka ne, wacce kake mora kullum, wacce take maka hidima kullum? Dole ne ka bata hakkin ta.


Dole ne idan za ka yi aure kayi la'akari da irin wannan abubuwan. Kar kaje ka dakko yarinya mai daraja kuma kazo ka kashe ta. Tun tana hakuri har sai ka sata ta fara maula, da roko a cikin yan uwa. Wata kuma ta fara neman Exes din ta su zo su taimaka mata. 


Ance daidai ruwa daidai tsaki. Idan kana da manmako ko baka da karfi to ka auri irin ka yar gida Malam Shehu. Manzon Allah SAW yana cewa cikin wani Hadithi, idan a gidansu yarinya tuwo take ci, to ka bata tuwo, idan su yan kwai da madara ne toh ka bata. Kar ka rabo ta da jin dadi, kuma ka kasa bata jin dadi. Shi aure transfer of ownership ne. Ka karba daga wajen mahaifin ta, yanzu kaine sabon mahaifi a wajen ta.


Don Allah a gyara.

A rika kulawa da mata da bukatun su. Ba'ace kayi kullum ba. A'a, time to time. Idan baza ka iya ba toh ka hakuri don zaka cutar da yar mutane. Sannan idan anayi musu kadan a rika hadawa da hakuri. Kayi ta bata hakuri, Kuma ka rika nuna sympathy and remorse lokaci zuwa lokaci.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post