Maza Gareku: Ku guji yin soyayya da mata masu irin wannan halayen - Android PolsKa nisanci yin rayuwa da duk wata mace dake da wadannan halayen. 


Wasu mazan suna cikin dangantaka ta soyayya mai guba amma suna jin a ransu hakan ba abin damuwa bane. Sai dai akwai wasu dabi'un da ya kamata Idan mace tana yi muku su ku yi watsi da ita domin bai kamata ku jure zama da macen dake da irin wannan dabi'u ba. A shawarce zai fi kyau ku kauracewa mace idan kuka gano suna da irin wannan halayen. 


Duk irin yadda ka kai da son mace Ka guji yin dangantakar soyayya da ita idan tana yin waɗannan halayen kamar haka;


1.Mace mai yawan abokai maza. 

Macen da ta yarda da zama da abokai maza fiye da kawaye mata, ya kamata a guji yin soyayya da ita. Domin ba za ta iya ba ku kulawa da ya kamata ba domin ta riga ta saba da abokanta maza da suke iya bata dukkan wata kulawa da take bukata. 


 2.Mace mai yawan zuwa unguwa. 

Fita unguwa ba abu ne mai laifi ba, amma duk macen da za ka ganta kullum a hanyar zuwa unguwa to ba abokiyar rayuwa bace domin kuwa akwai rashin kamun kai a tare da ita. Don haka idan kana da budurwa mai irin wannan halin ka rabu da ita. 


3.Macen da ba ta girmama ka.

 Girmamawa yana daya daga cikin muhimman abu dake Kara sa kaunar mai girmamawa ga wanda ake girmamawa. Matar da ba ta ba ka darajar da ta dace bai kamata ta kasance a rayuwarka ba. Mutum na gaske ya cancanci girmamawa. Don haka ku guji soyayya da matar da ba ta girmama ka.


Da fatan mata masu irin wannan halayen za su yi hankali su kiyaye kuma su gyara irin wannan halayen marasa kyau da suke aikatawa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post