Na sha fadi, kashi 80 na matan da suke kukan maza sun yaudaresu da zaka zauna ta baka labarin yadda akayi sai ka fahimci laifinta ne.
Duk kuwa da akwai wasu halayen mata da dabiunsu da su kansu ba zasu iya kauce musu ba sai wacce Allah Ya kare. Sai dai kina iya amfani da hankalin da Allah (SWT) ya baki domin amfanar kanki da kanki.
Ga wasu abubuwan da za ki kauce aikata su muddin baki son nan gaba ki soma kukan an yaudareki, ga abubuwan kamar haka;
1: Kada ki matsawa saurayi ko duk wani namiji da ya nuna miki soyayya. Matsawa irin na yawan kira da tura sakonnin text a farko-farkon fara soyayyar ku. Daure ki rabu dashi idan ya kiraki ki dauka, kuma kada ki nuna masa rashin kiranki da baiyi ba ko ba yayi da wuri yana damunki. Kuma kada ki bari hakan din ya dameki.
2: Ki guji neman yin kusanci da shi yadda zaki manne masa ko makalemasa. Nunawa namiji wannan mannau din da yawan shiga duk inda yace ku shiga zai iya zamemiki illa a nan gaba. A kullum kada ki nunawa saurayi soyayyar da kike yi masa zai iya sa ki bishi duk inda yake bukatar ki bishi ko ki shiga da shi.
3: A kullum yi kokarin nuna masa ba shi kadai ke sonki ba, ba kuma sai da shi zaki iya rayuwa ba. Ki rika kokarin cusa masa shakku a zuciyarki na ko baki sonshi ne.
4: Kada ki zama mai neman wani abu daga gareshi. Kada ki sake ki nuna masa talauci da gazawarki domin ya baki kudi ko taimaka miki.
5: Kada ki kauda kai ko yin shuru akan duk wani abu da yai miki ko ya furta miki da baki ji dadin abun ba. Nuna masa rashin dacewar hakan, da kuma fatan zai kiyaye nan gaba.
Nemawa kanki mutunci a wajen namijin da yake sonki da aure tun a farko-farkon soyayya ake yin hakan ba sai kun zama jiki ba.
Da zaran kinyi sakaci da wasu abubuwan a tun farko, ke abun zai wahalar a nan gaba.
Da fatan mata musamman 'yan mata zaku kiyaye.