Saiwar Zogale na dauke da Sinadaran dake da matukar muhimmanci musamman ga lafiyar dan adam. Ga wasu daga cikin amfanin da yake yi da ya dace ku sani kamar haka.
1Sanyin kirji:
A tauna saiwar zogale tare da citta kwara daya.
2 Tsutsar ciki:
A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.
3 Ciwon sanyi ga mata da maza:
A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.
4 Yawan ruwan maniyi ga namiji:
A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.
5 Tarin sanyi ko Mura: A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.
6 Rage nauyi ko kiba:
A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum
7 Zafin fitsari:
A tafasa saiwar zogale da kanumfari a sha sau uku safe da rana da yamma.
8 Ciwon sugar:
A rinka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.
9 Karzuwa:
A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha.
10 Ciwon daji a cikin baki:
A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dashi a kullum sau uku, safe da rana da yamma
11 Ciwon yatsa na Dankankare :
A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.
12 Matsanancin ciwon kai na zafi:
A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.
13 Ni'ima ga mata:
A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin Kofi sai a zuba rabin gwangwanin madara a sha.
Da fatan Allah yasa mu amfana daga wannan fa'ida dake tattare da Saiwar Zogale.