Wata marubuciya mai suna Aseeya Muhammad ta bayyana wasu dalilan da take ganin su ke janyo mutuwar Aure a wannan zamanin da muke ciki.
Daga Aseeya Muhammad Omar.
Abun akwai damuwa yadda ake ta samun yawan mace macen aure a wannan zamanin da muke ciki.
Wani auren bai fi ayi watanni dayi ba idan ma yakai, zakaji an fara samun matsalolin tsakanin ma’auratan daga nan kuma sai dai aji mutuwan auren.
A wannan zamanin da muke ciki
(1) Rashin girmama juna: yana taka muhimmiyar rawa wajen mutuwar aure zakaga mace bata ganin girman mijinta shima mijin baya ganin girma da darajar matar dole za’ayi ta samun matsaloli wadanda za su kai ga rabuwa.
(2) Karya: tana cikin abinda yake kawo mutuwar aure saboda an gina neman auren akan karya. misali namiji bazai fadawa mace asalin shi waye ba da kuma ainihin sana’ar sa, sai ya daura ta kan karya ya nuna mata shi wanine.
Bayan aure idan ta fahimci shi asalin waye anan ne za’ayi ta samun matsalolin da zasu kai ga rabuwa.
(3) Gasa: tana taka rawa wajen mutuwar aure. zaku ga namiji bashi da karfin rike mata amma saboda yaga abokansa sunyi aure shima sai yace sai yayi, bayan aure za’a zo bazai iya daukar nauyinta ba wani ma ko ciyar da ita bazai iya ba dole aure ya mutu.
Ita kuma wata macen mijinta yana daukar nauyin ta daidai gwargwargo amma tasa gasa a ranta sai ta yi abinda kawaye sukeyi sai ta sa sutura mai tsada da sauransu, shikuma miji bai da karfin haka.
(4) Kazanta da rashin iya girki: suma suna cikin jigo dake haddasa mutuwar aure. Anyi aure mace baza ta iya gyara jikinta da muhallin da take ciki ba gashi bata iya girki ba dole aure zai samu matsala.
(5) Kwadayi: shima kwadayi yana taka rawa wajen rugujewar aure a wannan zamanin.
Saboda watakila mijin yana son matar ne ba don Allah ba sai dan kwadayin dukiyar iyayenta idan akai aure yaga bai samu abinda yakeso ba daga nan za’a fara samun matsala.
Itama macen tayu sbd kwadayi wani abu da take zaton mijin nada shi take son mijin da anyi aure ta gano bashi da wannan abun daga nan zasu fara samun matsala.
(6) Rashin hakuri: shima yana taka rawa wajen rugujewar aure kowanne bazai yi hakuri da kowa a zauna lafiya ba.
(7) Rashin kulawa: rashin kulawa ta bangaren ciyar wa, da sutura da kuma rashin kulawa da halin da mata take ciki.
Wani idan ya saka kafa ya fita tun safe bazai dawo ba sai dare ba ruwan shi da ya bincika yaji halin da matar sa ke ciki.
Suma mata ana sun bangaren rashin kulawa da miji kan janyo matsala a auren ba ruwanki da halin da mijinki ke ciki idan kinga sauyawar yanayi a tare da mijin bazaki bincika kiji matsalar sa ba.
A bangaren wasu iyayen rashin barin yara su zabi abokanan rayuwar su da kansu yakan taka rawa wajen rushewar aure zaku ga namiji nemo matar da yakeso ya aure amma iyayen shi zasu ce bazai aureta ba batare da wani dalili ba.
Itama kuma a bangaren mace za’a hanata auren wanda take so. Daga nan idan akai aure kowa baya son kowa wasu ma musgunawa junan su zasu yi tayi saboda basa son juna daga nan har a rabu.
Gaskiya labarin yy Allah yasakada Alkhairi
ReplyDelete