Abubuwan da suke janyo hankalin mata su faɗa soyayya da namiji - Android Pols



Saɓanin maza waɗanda su a duk lokacin da suka zo neman aure kyau shine abu na farko da suka fi baiwa muhinmanci, amma su mata kyan jikin namiji bai cika sa mace ta faɗa soyayya dashi ba (ba wai nace mata basa la'akari da kyan jikin maza bane sam-sam) amma iya kula da ita da kuma yaranta yafi muhinmanci a gareta fiye da kyan jiki.


Kamar yadda masana suka ce, "mata sun fi son mazaje waɗanda suke da ƙarfin iya basu kariya (wannan ya haɗa da mazaje masu dukiya da kuma ƙarfin hali ko zarra) kuma waɗanda suke da ƙarfin gwiwar iya yi musu magana ba tare da fargaba ba. 


Don haka abun da wannan binciken yake nunawa shine mata sun fi mayar da hankali akan matsayin da mutum yake dashi a cikin al'umma, ƙarfin dukiyar shi ko kuma idan akwai yuwuwar zai iya yin arziki wata rana.


Kyan jikin namiji bai cika sa mace ta faɗa soyayya dashi ba, a maimakon haka, iya bada kariya da kuma iya ciyar da ita da 'ya'yanta yafi muhimnmanci a gareta fiye da kyan jiki da fuska. Amma duk da haka a wasu lokutan matan suna yin la'akari da jikin mutun, dama wasu alamun ƙarfin iko da arziki dake nuna cewa mutun zai iya karewa da kuma kula da iyalen shi. 


Abubuwan da matan ke dubawa sune tsafta da kuma sanya sutura mai kyau, riƙe babban muƙami a wata ma'aikata ko a cikin al'umma, mallakan abubuwa masu tsada kamar mota mai tsada, sutura mai tsada, waya mai tsada da dai sauran su dake nuna cewa mutun yana da arziki mai tarin yawa.


Amma ba duka mata ne suke da wannan tunanin ba, da fatan an karu daga wannan darasi mai muhimmanci. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post