Abubuwa 12 Da Mace Ke Siffanta Dasu Idan Tana Son Ka So Na Haƙiƙa - Android PolsIta mace ba kamar namiji bace wajen soyayya domin ita idan tana son namiji a Zahiri take nunawa, kuma komai tana Iya yi akan wannan soyayyar da take yiwa namiji.


Kuma duk mace idan ta Kamu da soyayyar namiji akwai wasu abubuwa da take yi don jin kai ga wanda take so. Ga abubuwan kamar haka ;


1. Tausayi :- Idan mace na son ka za ta rika matukar tausayama da ɗaga ma ka ƙafa a dukkan al'amuranka musamman abinda ya shafi dawainiyar kudi. 


2. Rufama asiri :- za ta kasance mai boye duk wani aibinka ga mutane, da yin wasu dawainiya dan kar a ga gazawarka, da ƙoƙarin nunawa mutane ƙoƙarinka boye wasu laifukan da kake aikatawa kamar shaye-shaye, neman mata, kallon fina-finan banza, chatting din batsa ko exchanging na nudes da ta gani, ko kana dukanta ko baka sauke wani hakkin ta, rauninka a shimfida, da sauransu. Ya kan yi wuya in mace na sonka ta bude wadannan sirrukan in ba abu ya ci tura ba. 


3. Kare martabanka :- duk wani abinda zai sa wani ya rainaka ko ya jawoma ƙasƙanci a idon mutane za ta kiyaye kuma ta karema shi a idon kowa wani lokaci har tayi faɗa da 'yan uwanta akan ka. 


5. Burgeka :- duk abinda za ta yi ko ta koyo dan ta burgeka za ta yi, kama daga kwalliya, rangwada, gyaran gida da na jiki, girke-girke, da sauransu.


6. Son kyautatama da 'yan uwan ka :- za ta so yima abubuwa da zai kyautata mu'amalar ta da kai, takan kasance mai son yiwa 'yan uwanka kyauta. 


7. Samar ma farin ciki :- farin cikinka shine farin cikin ta, za ta kasance duk wani abinda za ta yi dan taga farin ciki a fuskarka za ta yi ko da kuwa wani lokacin za ta takura, amma babban burinta shine tagan ka cikin farin ciki wadda wannan ya fiye mata komai. 


8. Hakuri :- za ta kasance mai hakuri, kawaici, yafiya da yawan yi ma uzuri akan kuskuren da kake yi mata, ba ta barin matsalar dake tsakanin ku ya bunƙasa har ya zama sa6ani


9. Girmamawa :- ta san girma da darajarka, duk yadda kake ta san kaine jagoranta takan matukar kiyaye duk wani abinda zai sa kaga kamar ta rainaka. 


10. Duban kyawawan dabi'un ka :- kullum a cikin yi maka uzuri take yi wadda hakan ya ba ta daman duba zuwa ga kyawawan dabi'un da kawaici akan wadanda basu da kyau, domin son da ta ke yi maka yakan hanata ganin laifin ka ko munin wasu dabi'un ka.


11. Yin biyayya :- ta kan yi iya kokarinta wajen kiyaye abinda ta san kake so ayi, da kiyayewa da guje abinda ba ka so domin ba ta son abinda zai ɓata ma rai.


12. Son 'yan uwanka :- za ta kasance mai son 'yan uwanka da gyara mu'amalar dake tsakanin ka da su, za ta dauke su tamkar 'yan uwanta domin tasan su wani sashine na abinda take so. 


Wannan sune abubuwa 12 da mata ke yi idan suna son namiji, da fatan maza wanda mata ke nuna musu kauna za su daraja su da mutunta su.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post