Abubuwan Da Ke Kawo Faduwar Gaba Ga Dan Adam - Android Pols
Na kasance a kodayaushe gabana yana yawan faduwa, wani lokaci ma sai na rike kirjina. Shin wannan matsala ce ko kuwa?


Amsa: 


Faduwar gaba na faruwa ne yayin da zuciya ta fara bugawa da sauri-sauri, abin da Hausawa ke kira dukan uku-uku. Amma a likitance dukan uku-uku a zuciya shi ma wani abu ne daban, wanda ke nuni da ciwon zuciya kadai. 


Amma ita faduwar gaba akwai abubuwa da dama da kan jawo ta. Wato duk da cewa a al’adance abubuwan ban tsoro ne aka fi dangantawa da faduwar gaba, akwai matsaloli da dama, a likitance, da kan jawo hakan. Dukkan matsalolin zuciya kan iya sawa ta yi bugu cikin sauri, sai mu ji shi a matsayin faduwar gaba. Muhimmin abinda kan jawo hakan ke nan shi ne ciwon zuciyar shi kansa.


Wato ciwon zuciya shi ne farko a cikin jerin matsaloli masu kawo faduwar gaba. Ga yadda abin yake:


Zuciya dai tana daya daga cikin manyan sassan jiki, wadanda idan aikinsu ya tsaya, to rayuwa ma za ta tsaya. Takan buga sau 60 zuwa 100 a minti guda (ka sa hannunka a saman wuya gefen makogwaro, bangaren dama ko hagu, za ka ji irin bugun da wata babbar magudanar jini da ta fito kai tsaye daga jikin zuciya ta nufi kwakwalwa ke yi. Ka sa hannun agogo ka auna yawan bugun a cikin minti daya. In ta buga fiye da sau 100, to alamar akwai matsala ke nan, haka ma in ta buga kasa da sau 60). Akwai ciwukan zuciyar da ke nan kan sa faduwar gaba, akwai kuma wadanda kan sa bugun ya yi kasa.


Sauran abubuwa da kan jawo faduwar gaba, wadanda su ma bugun zuciyar suke karawa, sun hada da ciwon makoko, sai kuma rashin jini sosai a jiki, sai yawan shan kayan shaye-shaye irin su coffee da ganyen shayi sosai, da yawan zukar hayakin sigari, sai kuma wasu magunguna kamar na asma, da aiki ba hutawa da yawan shan magunguna barkatai, ba tare da ka’ida ba.


Shi makoko, babban abinda yake kawo shi shi ne girman wata ’yar halitta da ke manne da makwogaro ta waje, wadda muke kira thyroid gland, wanda fatar wuya ta lullube. Ita wannan halitta, a wasu lokuta, haka kawai takan samar da wani sinadari wai shi thyrodine, wanda ke aiki a jiki. To idan aikinsa ya wuce misali, har zuciya yake tabawa. Wannan sinadari na da amfani, idan yana jikinmu daidai wa daida, amma da ya fara yawa zai zama rashin lafiya. 


Za a ga idanuwan mai matsalar sun yi kwala-kwala, kuma ga yawan faduwar gaba da rawar jiki da ta hannaye da yawan jin zufa. Sai an ba da magunguna ko an yi tiyata a cire wani bangare na halittar, sa’annan abin ke Sauki. Shi rashin karancin jini shi ma dai zuciyar yake tabawa, tunda da ma aikin zuciya ya danganci buga jini ne, idan jini ya yi karanci a jiki, sai zuciya ta fara bugawa da sauri don ta cimma burin aika jinin yadda ya kamata.


Banda wadannan, sai aiki akai-akai ba hutawa, shi ma zai iya sa mutum yawan faduwar gaba. Wadanda suke aiki mai yawa, sun fi shiga hadarin amfani da magunguna masu rage gajiya da yawan shan kayan shayi masu rikita jiki, wadanda duk suna kawo faduwar gaba da rashin natsuwa, ta yadda ko barci ma gagararsu yake, a mafi yawan lokuta.

Har ila yau akwai kuma shi kanshi ciwon tsoro, wanda ya fi yawa a yara ko ’yan mata, wadanda sukan samu fargaba idan suka shiga jama’a, ko idan suna magana a cikin taro.


Da ma dai akwai mutanen da Allah Ya halicce su da saurin firgita, akwai kuma wadanda kwata-kwata ba su da tsoro, kuma wadannan akan kira su a Hausance “masu dakakkiyar zuciya”. Mai wannan matsala ta yawan faduwar gaba yana bukatar a caji lafiyar jikinsa gaba daya domin a gano dalili a ba da magani, kafin karamar matsala ta zamo babba. 


Tambaya :


Likita ko za a yi mana bayani a kan hanyar kariya daga zazzabin Ebola? Kuma da gaske wanka da ruwan gishiri kan iya magance ta?


Daga Ummu, Katsina


Amsa: Tun watanni hudu da suka shige, a farkon samun labarin bullar wannan annoba a kasashen Gini da da Saliyo da Liberiya, muka bayyana yadda za a kare kai da ciwon. Babban abin da muka zayyana a wancan lokaci, tun kafin zuwan ciwon kasar nan, shi ne na dakatar da masu shigowa wannan kasa daga kasashen da annobar ta bulla na dan wani lokaci, har sai matsalar ta lafa, amma hukumomi ba su yi haka ba. 


Muka ba da misali da kasar Saudiyya a lokacin, wadda ita ta dakatar da ba da takardar izini don shiga Umara, kuma har yanzu suna kan bakansu. Kin ga ke nan an dan samu sakaci mu ta bangaren namu jami’an da suka bari wani dan Saliyo, mai alamun ciwon, ya shigo kasar nan. Su kasashen Yamma da suke barin ’yan wadannan kasashe su shiga kasarsu, sai an bincike su, kuma su a shirye suke ko da irin wannan matsala za ta shigo musu.


Sauran abin da za mu iya yi a daidaikunmu shi ne kai rahoton duk wani mai alamu na mura, wanda ya dawo daga wata tafiya, ga hukumomi mafi kusa; yawan wanke hannaye da sabulu da yawan tsabtar muhalli. Tunda ciwon a Ikko ya bulla, sai mu guji zuwa Ikko a yanzu na dan wani lokaci.


Su kuma makiyaya da maharba da mafarauta, wadanda rayuwarsu ta fi yawa a daji, sai a ce su yi hankali da naman da sukan kama na daji a dan wannan lokaci domin dabbobi masu dauke da wannan kwayar cuta za su iya shigowa daga kasashen da ake annobar. Ba biri da jemage ba, har beran daji da gafiya da buzuzu da zomayen daji duka a wannan lokaci ya kamata a guji cinsu, har sai annobar ta lafa.


Sauran ma’abota sayen naman mafarauta ma sai su yi hattara a wannan dan lokaci. Cin alade ga masu ci, a wannan lokaci ke nan shi ma sai an yi taka-tsantsan, inji hukumar lafiyar.


Babu kanshin gaskiya da ake cewa idan mutane suka yi wanka da ruwan gishiri za su samu kariya daga ciwon. Wadanda ma suka yi haka ko suka sha ruwan, tuni an kai su asibiti saboda illar abin da suka sha din, wasu daga cikinsu ma sun kwanta dama.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post