Yadda Za Ka Gane Tsantsar Soyayyar Gaskiya Da Mace Ta Ke Yi Maka - Android Pols


A lokacin da kake kokarin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai bukatar ka nazarci wasu abubuwa wadanda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.


Farkon Haduwar ku

A yayin gabatar da soyayyarka a gare ta shin ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana soyayyarka a gareta?

Mafi yawancin mata abune mai matukar wahala a yayin da saurayi ya gabatar da soyayyarshi a garesu a karan farko su iya  furta kalaman amincewa ga wanda ya nuna yana son su. 


Saboda mafi yawancinsu sukan ji kunyar furta kalaman da suka dace ga wanda ya nuna yana sonsu a karon farko. To amma zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomin da suke nuni da SO.


Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar taku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani wanda ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya dauke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kudinka.


A saboda haka akwai bukatar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauransu lokaci bayan lokaci. 


A duk lokacin da ka bukaci mace ta baka amsar amincewa tana son ka sai kaga ta yi murmushi ko ta kasa furta wasu kalaman da suka shafi soyayya a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na so domin kuwa wanda ake so ake jin kunya. 


Kar ka damu game da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai kawai ka lura da wadannan abubuwa kamar haka;


1) Sau nawa kake kiranta a waya kafin ta amsa kiran naka?


Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba to zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu a bisa dalilin rashin amsa kiranka a kira na farko, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zaran ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.


2) Matukar tana son ka za ta kasance mai karbar duk wata shawarar da zaka bata kuma za ta kasance mai son abun da kake so.


3) A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna kosawa da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa lokacin da za ku yi sallama. 


4) Idan har ka saba kiran ta a waya muddun ta damu da kai idan ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka ta ji ko lafiya, idan ma bata Kira ba saboda wani dalili bayan ka kira za ta yi kalaman da zasu nuna tayi kewar ka.


5) Idan har tana son ka a kullum za ta ke kokarin yin abun da zai faranta ranka, za ta ke kokarin guje wa abun da zai sa ka yi fushi.


6) A lokacin da soyayyarku ta yi nisa za ta iya bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe ta.


7) A lokacin da ka nuna bacin ranka a kan wani abun da ta aikata ba dai- dai ba, a yayin baka hakuri da shawo kan ka za ta iya zubar da hawaye.


8) Zata ke kokarin bayyana ka ga kawayenta da kuma yan gidansu.


9) Zata ke kokarin turo maka da kalamai na soyayya.


10) Zata kasance mai tambaya a dangane da yan uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani da ta san kuna a tare.


11) Za ta ke damuwa da damuwarka. 


Irin wadannan abubuwa da sauran ire-iren su duk zai kasance ta na nuna maka su.


Yanayinta Da Kuma Halayyarta

Akwai bukatar ka fahimci yaya yanayinta da kuma halayyarta suke,


1) Shin tana da jan aji ne da yawa? wanda hakan ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu abubuwa da zaka iya tinanin wulakanci take yi maka, amma da sannu matukar ka iya allonka to zaka wanke.


2) Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana son ka, idan ka yi hakuri da sannu soyayyarka za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da sannu tulu yake fashe wa.


3) Koda a ce bata da son kudi farkon soyayyar ku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta son abun hannunka zai rinjayi son da take yi maka na gaskiya, wai ance kyauta tana kara soyayya, amma kuma komai yai yawa to zai kawo matsala. Wannan shi ne abun da zan iya cewa a ta’kaice.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post