Manyan Dabi’un Da Mata Ke Yi Da Ke Kashe Musu Aure - Android PolsDabi’un Mata 5 da suke aikatawa a gidajen aurensu wanda ke jawo mutuwar aure gabaki daya. 


Kamar yadda muka alkawuranta a makon da ta gabata cewa, zamu kawo wasu daga cikin dabi’u masu lalata aure a bangaren mata, mun ciki alkawari domin ga su kamar haka. Mata suna da matsaloli da yawa wanda yake kawo masu lalacewaar aurensu, daga cikin dabi’un dai akwai:


1. Kwadayi: Da yawa daga cikin mata su kan auri mutum don kwadayin wani abu da ke hannusa, wannan abun shi ne dalilin da ya sa suka yi aure. Bayan an yi aure sun je gidan mijin, za su tsaya su tabbatar da cewa wannan abun da suke so suna samun shi.


Idan kuma ya zama ba su samu ba, to za su ta da hankali a kan cewa sai an sake su, wasu kuwa ko da sun samu to duk sanda aka ce wannan abun babu shi ko kuma ya kare to haka suma zaman su da kai ya kare domin abin da ya kawo su ya kare.


2. Rashin Biyayya: Mata da yawa ba su da biyayya wanda shi kuma namiji yake bukata, sakamakon haka dole ne aure ya rabu saboda rashin zaman lafiya.


3. Rashin Iya Kwalliya: Rashin iya kwalliya da kuma ado yana kawo rabuwar aure, saboda shi namiji yana son ya ga matarsa cikin kwalliya a kowanni lokaci. Za ka iya samu cewa miji ya kawo duk abin da ake bukata na kwalliya, amma ita kuma matar ba ta yi, to sai ka ga ya fi bukatar zama a waje fiye da cikin gidansa domin sai matarsa ta daina birge shi, daga nan sai yawan fada, sai kuma rabuwa wanda wannan laifin mata ne.


4. Rashin Iya Girki: Da yawa daga cikin mata ba a koya masu girki a gidajensu wanda sai sun yi aure sannan abun ya zamar masu matsala. Rashin iya girki babbar matsala ce a zaman aure wanda za ka samu cewa duk abin da mace ta dafa babu dadi ko kuma ba a iya ci, shi kuma mai gidan yana kawo duk abin da ake bukata wajen girki amma babu biyan bukata wajen girki wanda daga karshe idan ya gaji sai ka ga ya sake ta wanda wannan matsalar mace ce.


5. Iya Magana: Wasu matan ba su san yanda za su yi magana da mijinsu ba, sai ka samu cewa ga matar da matukar kyau amma mijin baya gani saboda rashin iya magana.


Da fatan mata za su gyara halayyarsu da suke yi a gidajen mazajensu domin zaman gidan miji yafi komai rufin asiri. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post