Wasu Dalilan Da Za Su lya Jawo Mace Ta Fasa Aurenka - Android Pols


Za'a ga masoya sun yiwa juna alkawarin aure, amma kuma daga bisani sai macen ta sauya ra'ayinta ta fasa auren.


Hakan yasa maza da yawa suke zargin mata da yaudara, wanda a zahiri abun ba haka yake ba. Akasarin idan irin wannan ya faru idan za'a yi bincike sosai za a fahimci shi namiji shine da laifi.


Ga wasu dalilai da muka tattaro muku dake jawo mace tace ta fasa auren namiji koda kuwa ya kai kudin aure gidan iyayenta. 


1: Mata masu nutsuwa suna duba namijin da za su aura wani irin namiji ne shi, Ma'ana wajen tsari da burin da yake da shi a rayuwa.


Daga lokacin da mace ta gano kai namiji ne wanda ba shi da buri ko bai san ciwon kansa ba. Daga wannan lokacin za ta sauya tunanin ta gareka.


Mace tana son ganin namiji mai buri da kokarin neman na kansa ba dogaro da wani ko wasu ba. Don haka mace na iya fasa aurenka idan ta gano kai cima zaune ne.


2: Idan mace ta gaji da jiran namiji akan maganar aure tana iya fasa aurensa koda kuwa batada wanda za ta aura.


Ita mace tana son a lokacin da ka furta mata zancen aure ya kasance a shirye kake. Idan Kuma ka nemi uzurin akai auren zuwa wani lokaci duk za ta amince. Amma daga lokacin da ta fahimci bakada magana daya tana iya fasa aurenka.


Kada kayiwa mace alkawarin aure bakada tabbas akan lokacin yin auren. Domin ita mace duk yadda take ba Kai kadaine ke sonta ba. Mace mai manema a kullum tana cikin barazanar shedan ne na rabuwa da wanda take so ta kama wanda ya fishi.


Don haka ka guji jawowa wacce ka yiwa alkawarin aure rai ba tare da dalilai masu karfi ba.


3: Daga lokacin da mace ta fahimci wani abu da baka dace ka zama mijinta ba ko gobe ne za'a daura muku aure da ita tana iya fasawa.


Akwai wasu maza mayaudara ko makaryata da suke nuna karyar arziki. Sai kuma daga baya budurwa ta gano kamin daurin auren.


Kaje wa mace a mutum. Mace shu'uma ce. lya gaskiyar ka wajenta iya yadda kake shiga ranta.


4: Mace idan ta hadu da wanda ya fika tana iya sauya shawaran aurenka. Ba ana nufin ya fika kudi ko matsayi ba.


Mata na son kulawa. Da zaran mace ta fahimci wanda ta hadu dashi ya fika kulawa da sakin fuska da iya soyayya da wayewa da bata 'yanci, yanzu nan za ta iya sauya ra'ayinta game da Kai akan auren da kuka yi alkawari.


5: 'Yan uwa da abokan mace suna da tasiri akanta wajen cusa mata ra'ayi. Idan akayi dacen wacce kake son ka aura tana suraron shawara daga yan uwanta ko abokanta suna iya sauya mata tunani game da kai musamman idan akayi rashin dace taku bai zo daya ba.


Kada kayi tunanin za su zo mata da Kalmar ta rabu da kaine kawai ba tare da kawo mata misalan da za su gamsar da ita ba.


Kamar yadda kake so wacce za ka aura ta samu kyankyawan fahimta da yan uwanka da abokan ka, kaima yana da kyau ka samu hakan da nata idan ba haka ba suna iya sauya mata ra'ayi a kanka.


Da fatan maza masu soyayyar neman aure za su hankalta. Kamar yadda maza suke sauya ra'ayi akan auren macen da suka yi mata alkawari, haka suma mata suke.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post