Hadin Karawa Mace Ni'ima Da Sha'awa Da Karin Dandano - Android PolsMatan Aure Kawai, Idan kun karanta ku yi kokari ku turawa sauran yan uwa domin suma su amfana. 


Wata fa'ida ce wacce kamata yayi kafin na fada, kowacce mace da za ta yi amfani da ita ta bani wani tukwici amma saboda mai gida na bar muku shi kyauta. 


Macen da ke so ta rikita mai gida ga hanya mai Sauki, ke ko mota kike so indai kikai wannan hadi tofa kin samu, amma fa idan an samu mota kar a manta dani. Hanyar kuwa itace. 


 Zaki Samu wadannan abubuwan kamar haka:


 1. Dabino 

 2. Kwakwa (coconut) 

 3. Nonon Rakumi 

 4. Zuma


 Yadda Zaki Hada shine kamar haka :


Da farko zaki cire kwallon dake cikin dabino,sai ki kawo kwakwar ki bayan kin bare bawonta ki samu ruwa kadan ki zuba a kai kiyi blending nasu.


Bayan kin gama sai ki kawo zuma kamar rabin kofin nonon Rakumi kamar kofi daya ki hada da kwakwar nan da kika hada da dabino ki hade da zuma da nonon Rakumin waje daya. 


Ki rika sha kadan-kadan kamar tsawon kwana 7 zaki bada labari.


Hadin Zuma:

Karin ni’ima da motso sha’awa, za ki sami zuma mai kyau ki zuba garin habbatus-sauda da man zaitun ki juye su guri guda sai ki dinga sha babban cokali biyu da safe da kuma yamma.


1. Zuma 


2. Garin habbatus Sauda 


3. Man zaitun 


Hadin Danyan Kwai:

Yana karawa mace kuzari ba tareda ta gajiya ba wajen jima’i kuma yana karawa mace ni’ima da sha’awa. Ki samu wadannan abubuwan kamar haka:


1.lipton 


2. Danyen kwai 


3. Zuma 


A jika lipton da ruwa kadan har sai yayi baki, sai ki fasa kwai ki hada shi, sai ki zuba a cikin ruwan lipton kina iya zuba madara peak sai ki zuba zuma ki dinga sha.


Karin Ni'ima:

Zaki iya yin shayin kara karfin sha'awa da ni'ima yadda za ki yi shine ki samu sassaken baure ki dakashi sai ki daka kanunfari ki hada da lifton kina sha Za ki yi mamaki musamman idan ke matar aure ce. 


Da fatan wannan hadin zai amfanar da dukkan matan da suke da bukatar hakan. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post